DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Thursday, September 24, 2026
HomeUncategorizedShugaba Tinubu ya tura Minista Badaru zuwa Neja don ganin an ceto...

Shugaba Tinubu ya tura Minista Badaru zuwa Neja don ganin an ceto daliban da aka sace

Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu ya umurci  Ministan Tsaron kasar, Badaru Abubakar, da ya tashi kai tsaye zuwa jihar Neja domin jagorantar aikin ceto daliban makarantar St. Mary’s Catholic School da ‘yan bindiga suka sace a yankin Papiri, ƙaramar hukumar Agwara.

Umarnin na zuwa ne sa’o’i bayan da kungiyar kiristoci ta Njeriya CAN reshen jihar Neja ta tabbatar da sace ɗalibai 303 da malamai 12 a makarantar, lamarin da ya kara tayar da hankalin al’umma a fadin ƙasar saboda ƙara yawan hare-haren da ake kaiwa makarantun Arewa.

Yawan hare-hare kan makarantun ya sa gwamnatin tarayyar kasar ta umurci da a rufe makarantun sakandare mallakinta sama da 40 a fadin kasar. Yayin da gwamnatocin jihohin Katsina da Plateau suka sanar da rufe nasu makarantun firamare da sakandare.

A baya-bayan nan, Shugaba Tinubu ya tura Ministan Ƙasa a ma’aikatar tsaro, Bello Matawalle, zuwa jihar Kebbi domin ganin an ceto dalibai 24 mata na Government Girls’ Comprehensive Secondary School, Maga, da aka yi garkuwa da su a ƙaramar hukumar Danko Wasagu.

Masu sharhi na ganin cewa tura ministoci biyu manya zuwa yankuna biyu daban-daban a lokaci guda na nuna yadda matsalar tsaro ta kara kamari, tare da bukatar sabbin dabaru da matakan gaggawa. Yanzu idanun jama’a na kan yadda gwamnati za ta gudanar da aikin ceto da tabbatar da tsaro a makarantun Arewa maso yamma da tsakiya.

Ukashatu Wakili
Ukashatu Wakilihttps://dclhausa.com
Ukashatu Wakili is a journalist and media professional serving as Deputy Managing Editor and Internship Coordinator at DCL Hausa. He has extensive experience in broadcast and digital journalism, with expertise in news reporting, editorial production, newsroom coordination and journalist training. He holds a B.Sc. in Mass Communication from Usmanu Danfodiyo University, Sokoto.
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata