Tsoffin jami’an ‘yansandan Nijeriya sun gudanar da zanga-zanga a ranar Litinin a birnin Abuja, inda suka nuna rashin amincewarsu da tsarin fansho na (Contributory Pension Scheme) CPS da ake amfani da shi a kansu bayan sun yi ritaya.
Rahotanni sun ce masu zanga-zangar sun taru ne a kusa da ƙofar Fadar Shugaban Ƙasa, inda suka riƙa ɗaga alluna masu ɗauke da saƙonni daban-daban, suna kiran gwamnatin tarayya da ta duba halin da suke ciki, kamar yadda Channels TV ya wallafa.
Sun bayyana cewa tsarin bai dace da aikin ‘yansanda ba, duba da irin haɗarin da suke fuskanta a lokacin da suke aiki.
Masu ritayar sun zargi tsarin fanshon da cewa yana jefa su cikin ƙunci da talauci, inda suka ce kuɗin da suke karɓa ba ya wadatar da su wajen biyan buƙatun yau da kullum.
A cewarsu, ya kamata a ware musu wani tsari na musamman kamar yadda ake yi wa wasu sassan gwamnati.
Bugu da ƙari, masu zanga-zangar sun buƙaci gwamnati da ta cire su gaba ɗaya daga tsarin CPS, tare da mayar da su cikin tsarin fansho na gargajiya, wanda suka ce zai fi ba su kariya da tabbacin rayuwa mai kyau bayan ritaya.
Wasu daga cikin masu zanga-zangar sun kuma nuna damuwa kan jinkirin biyan kuɗaɗensu da kuma yadda ake tafiyar da asusun fansho, lamarin da suka ce yana ƙara tsananta musu halin da suke ciki.
