DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Sunday, April 19, 2026
HomeLabaraiAl-Makura ya ce Gwamnan Abdullahi Sule bai tuntube shi ba kafin zaben...

Al-Makura ya ce Gwamnan Abdullahi Sule bai tuntube shi ba kafin zaben magajinsa na 2027

Tsohon Gwamnan Jihar Nasarawa kuma mai kula da yankin Arewa ta Tsakiya na ƙungiyar Renewed Hope Ambassadors, Sanata Umaru Tanko Al-Makura, ya ce Gwamna Abdullahi Sule bai tuntube shi ba kafin ya bayyana wanda yake so ya gaje shi a zaɓen gwamna na shekarar 2027.

Kamar yadda rahotanni suka nuna, Gwamna Abdullahi Sule ya bayyana Sanatan da ke wakiltar Nasarawa ta Yamma a Majalisar Dattawa, Aliyu Ahmed Wadada, a matsayin wanda yake so ya gaje shi, yayin wani taro da ya yi da masu riƙe da mukaman siyasa da shugabannin hukumomi a gidan gwamnati da ke Lafia.

DCL Hausa ta ruwaito cewa Sanata Al-Makura ya bayyana hakan ne yayin da yake zantawa da manema labarai a Lafia bayan wata ziyara da tsohon Sufeto Janar na ‘Yan Sanda, Mohammed Abubakar Adamu, wanda shi ma ke neman takarar gwamna a jam’iyyar APC, ya kai masa.

Al-Makura ya ce sanarwar da gwamnan ya yi ta wuri ne sosai, yana mai cewa jam’iyyar APC ba ta fara sayar da fom ɗin takara ba, don haka duk wani goyon baya a yanzu na iya kauce wa ka’idojin jam’iyyar.

Ya ƙara da cewa duk da cewa gwamna na da ‘yancin nuna wanda yake so ya mara wa baya, amma bai kamata hakan ya zama kamar an riga an yanke hukunci kafin a fara tsarin fidda ‘yan takara ba.

Shi ma tsohon Sufeto Janar na ‘Yan Sanda, Mohammed Abubakar Adamu, ya koka cewa wasu shugabannin jam’iyya a jihar sun riga sun nuna goyon baya ga Sanata Wadada, yana mai cewa bai kamata a tilasta wa jami’an gwamnati su mara wa wani ɗan takara baya ba.

Ukashatu Ibrahim Wakili
Ukashatu Ibrahim Wakilihttps://dclhausa.com
Ukashatu Wakili, Mataimakin Manajan Edita kuma Mai Kula da Shirin Koyon Sanin Makamar Aiki ne a DCL Hausa. A matsayinsa na ƙwararren ɗan jarida yana tsara ayyukan rediyo da kafafen sada zumunta, fassarar labarai, da tabbatar da sahihancin bayanai. Yana jagorantar shirin horaswa ga masu koyon aiki tare da kula da ingancin rubuce-rubuce da shirye-shiryen gidan jaridar.
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata