DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Sunday, April 19, 2026
HomeLabaraiMalam Ibrahim Shekarau ya fice daga jam’iyyar PDP

Malam Ibrahim Shekarau ya fice daga jam’iyyar PDP

Sanata Ibrahim Shekarau, tsohon gwamnan Jihar Kano kuma Sardaunan Kano, ya sanar da ficewarsa daga jam’iyyar PDP bayan shekaru yana cikinta.

Kamar yadda takardar murabus ɗin da ya aike wa shugabannin jam’iyyar a gundumar Giginyu da ke Ƙaramar Hukumar Nasarawa a Kano ta nuna, Shekarau ya ce ya yanke shawarar ficewa daga PDP ne daga ranar Lahadi 19 ga Afrilu 2026.

A hirarsa da DCL Hausa, hadimin Shekarau kan harkokin yaɗa labarai, Dokta Sule Ya’u Sule, ya ce rikicin cikin gida a jam’iyyar PDP ne ya sa Malam Ibrahim Shekarau da tawagarsa suka yanke shawarar neman mafita a wata jam’iyya.

Ya ƙara da cewa akwai shakku cewa jam’iyyar ba za ta tsaya takara yadda ya kamata ba, lamarin da ya sa aka kafa wani kwamiti a cikin ƙungiyar siyasar Shekarau wanda daga ƙarshe ya ba da shawarar a fice daga jam’iyyar.

Dokta Sule Ya’u Sule ya kuma bayyana cewa a yau Lahadi ne Malam Ibrahim Shekarau zai sanar da sabuwar jam’iyyar da shi da ‘yan majalisar shura suka amince za su shiga.

Ukashatu Ibrahim Wakili
Ukashatu Ibrahim Wakilihttps://dclhausa.com
Ukashatu Wakili, Mataimakin Manajan Edita kuma Mai Kula da Shirin Koyon Sanin Makamar Aiki ne a DCL Hausa. A matsayinsa na ƙwararren ɗan jarida yana tsara ayyukan rediyo da kafafen sada zumunta, fassarar labarai, da tabbatar da sahihancin bayanai. Yana jagorantar shirin horaswa ga masu koyon aiki tare da kula da ingancin rubuce-rubuce da shirye-shiryen gidan jaridar.
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata