DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Monday, September 21, 2026
HomeKetareAn zaman makokin kwanaki 10 bayan rasuwar ƙanin Sarki Dubai

An zaman makokin kwanaki 10 bayan rasuwar ƙanin Sarki Dubai

Sheikh Ahmed bin Rashid Al Maktoum, ƙani ga mai mulkin birnin Dubai, Sheikh Mohammed bin Rashid Al Maktoum, ya riga mu gidan gaskiya yana da shekaru 76 a duniya.

Jaridar Punch ta ruwaito cewa ya rasu ne a ranar Litinin, 21 ga watan Satumban 2026, kamar yadda ofishin yaɗa labarai na gwamnatin Dubai ya sanar ta shafinsa na dandalin X.

Biyo bayan rasuwar tasa, ofishin Sarkin Dubai ya sanar da kwanaki 10 na zaman makoki a hukumance tare da saukar da tutoci ƙasa a faɗin birnin Dubai domin girmama marigayin.

Sanarwar da ofishin ya fitar ta ce, “Cikin zuciya mai cike da tawakkali ga ƙaddara da hukuncin Ubangiji, ofishin Mai Martaba Sheikh Mohammed bin Rashid Al Maktoum, mataimakin shugaban ƙasa kuma firaministan UAE kuma mai mulkin Dubai, yana jimamin rasuwar Sheikh Ahmed bin Rashid Al Maktoum, wanda ya koma ga mahaliccinsa a safiyar yau Litinin. Ofishin ya ayyana zaman makoki a hukumance tare da saukar da tutoci a Dubai na tsawon kwanaki goma, daga ranar Litinin.”

Sheikh Mohammed ya fitar da saƙon alhini ga ɗan uwansa, inda ya bayyana cewa, “Allah ya yi wa Sheikh Ahmed bin Rashid Al Maktoum rahama. Allah ya ji ƙanka ɗan uwana. Yanzu ka koma ga Ubangijinmu, Mai Kyauta kuma Mabuwayi. Ka ɓace daga idanunmu Ahmed, amma ba za ka taɓa fita daga addu’o’inmu ko zukatarmu ba.”

Rahotanni sun bayyana cewa marigayi Sheikh Ahmed ya taɓa riƙe muƙamin mataimakin shugaban rundunar ‘yan sanda da tsaron jama’a na birnin Dubai. Ya kuma kasance fitaccen jigo a fannin tseren dawakai na duniya, inda yake da shahararrun dawakan tsere a Burtaniya da suka haɗa da Mtoto da Addeybb, tare da mallakar filin tseren dawakai na Jebel Ali da ke Dubai.

Ƙungiyar tseren dawakai ta Dubai (Dubai Racing Club) ta karrama marigayin kan gudunmawar da ya bayar tsawon shekaru da dama ga ci gaban wasanni da kuma hawan dawakai a Hadaddiyar Daular Larabawa.

Ukashatu Wakili
Ukashatu Wakilihttps://dclhausa.com
Ukashatu Wakili is a journalist and media professional serving as Deputy Managing Editor and Internship Coordinator at DCL Hausa. He has extensive experience in broadcast and digital journalism, with expertise in news reporting, editorial production, newsroom coordination and journalist training. He holds a B.Sc. in Mass Communication from Usmanu Danfodiyo University, Sokoto.
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata