Wani sabon bincike da ƙungiyoyin Mata Media Organisation da Mata Media Foundation suka gudanar ya bayyana cewa kashi 50 cikin 100 na mata ’yan jarida a Arewacin Nijeriya sun taɓa tunanin yin murabus ko barin aikin jarida gaba ɗaya, sakamakon yadda aikin ke yin tasiri ga lafiyar ƙwaƙwalwarsu da jin daɗin rayuwarsu.
Binciken mai taken “Silent Burdens, Shared Strengths: Understanding Mental Health, Stigma and Systems of Care Among Women Journalists in Northern Nigeria”, ya tattara ra’ayoyin mata ‘yan jarida 58 daga sassan Arewacin Nijeriya domin duba matsalolin takura a wurin aiki, yanayin lafiyar ƙwaƙwalwa, hanyoyin samun tallafi, da kuma rashin ingantaccen tsarin kula da ma’aikata a gidajen yada labarai.
-
Kashi 91% na fuskantar matsin lamba mai nasaba da aiki akai-akai.
-
Kashi 78% na fama da gajiyar ƙwaƙwalwa ko gundura (burnout).
-
Kashi 86% na fama da tarin aiki ko gajiyar yawan bayanai.
-
Kashi 50% (mutum 29 daga cikin 58) sun yi tunanin barin aikin jarida saboda yadda yake shafar lafiyarsu.
Rahoton ya ce babban abin damuwa shi ne yadda kashi 86% na matan suka bayyana cewa gidajen labaran da suke aiki ba sa ba da wani tsarin tallafi na kula da lafiyar ƙwaƙwalwa, ko kuma ba su da masaniya ko akwai irin wannan tallafin. Wannan ya sa mafi yawansu ke dogaro da yin magana da ƴan uwa, abokai, dagewa da addu’a, ko kuma nesanta kansu daga aiki domin samun sauƙi.
Haka kuma, kashi 69% na waɗanda aka tattauna da su sun nuna cewa ba sa jin daɗin tattauna matsalolin lafiyar ƙwaƙwalwarsu da editoci ko shugabannin wuraren aikinsu, sakamakon tsoron kada a kalle su a matsayin marasa ƙarfi, fargabar rasa aiki ko damammaki, da kuma rashin samun cikakkiyar yarda a tsarin gudanarwa.
Babbar Daraktan Mata Media Organisation, Fauziyya Kabir Tukur, ta bayyana cewa binciken yana nuna irin ƙalubalen da mata ’yan jarida ke fuskanta da yadda suke da matuƙar sha’awar aikin da kuma sadaukarwa ga al’ummarsu.
“Babban ƙalubalen da ke gabanmu a yanzu shi ne yadda za a sa aikin jarida ya zama mai dorewa ta yadda za su ci gaba da gudanar da aikinsu ba tare da sun sadaukar da lafiyarsu da jin daɗin rayuwarsu ba.”
Mata Media ta yi kira ga masu gidajen yada labarai, editoci, ƙungiyoyin ‘yan jarida, da sauran masu ruwa da tsaki da su samar da tsare-tsare na bai-ɗaya a ɗakunan labarai domin rage yawan lodin aiki, ba da damar hutu, bayar da horo kan lafiyar ƙwaƙwalwa, da kuma biyan albashi mai kyau.
