Wani direban ƙaramar motar ɗaukar kaya, Adeleye Adeniyi, haifaffen garin Ado-Ekiti, ya bayyana cewa ya ciwo bashin Naira miliyan 3.5 domin tallafa wa ƙoƙarin sake zaɓen Shugaban Ƙasa Bola Tinubu, shugaban masu rinjaye na majalisar dattawa, Opeyemi Bamidele, da ɗan majalisar dokokin jihar Ekiti, Steve Fatoba.
Adeniyi, wanda aka fi sani da laƙabin “Online Loan Man for BAO”, ya bayyana hakan a wata hira da ya yi da ’yan jarida, wadda bidiyonta ya yaɗu a ranar Juma’a, kamar yadda Jaridar Punch ta ruwaito.
A cikin bidiyon, ya nuna wani cak na bankin Wema da aka rubuta a kan kwali, wanda ke nuna cewa zai ware Naira miliyan biyu ga Tinubu, Naira miliyan ɗaya ga Bamidele, sannan Naira 500,000 ga Fatoba.
Ya ce a shirye yake ya fita ya yi wa ƴan siyasar kamfen gabanin zaɓuka masu zuwa, bisa abin da ya bayyana a matsayin ayyukan da suka gudanar a lokacin mulkinsu..
Ina talla ta shugaban ƙasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, domin burinsa na yin wa’adi na biyu. Na ciwo bashi. Ina son amfani da wannan kuɗi wajen tallafa masa saboda yana gudanar da ayyuka masu kyau ƙwarai,” in ji shi.
Adeniyi ya kuma yi alƙawarin fita kamfen domin Tinubu, inda ya ƙara da cewa: “Kamar yadda na sake faɗa, a shirye nake tsaf in fita domin yin kamfen ɗinsa. Zan kuma yi amfani da wannan wajen mara masa baya. A kan wannan wa’adi naka, za mu tsaya daram.”
Ya yi kira ga ƴan Nijeriya da su zaɓi Tinubu, Bamidele da Fatoba, yana mai cewa ya yi imanin Shugaban Ƙasar zai samar da ƙarin alfanun ga jama’a idan aka sake zaɓensa.
“Zan roƙi ’yan’uwana ’yan Nijeriya da mu nuna ƙauna ta hanyar ba shi damar yin wa’adi na biyu a kan mulki, domin har yanzu muna sa ran ganin abubuwa da yawa, fiye da waɗanda muka samu zuwa yanzu,” in ji shi.
Direban ya kuma yaba wa Bamidele da Gwamnan Jihar Ekiti, Biodun Oyebanji, kan gudummawar da ya ce suke bayarwa a fannonin kiwon lafiya, ilimi, samar da wutar lantarki da inganta ababen more rayuwa a yankunan karkara na jihar.
“Sanata Michael Opeyemi Bamidele, ina addu’ar Allah Ya kai shi ga babban matsayi. A lokuta da dama, idan na duba irin ayyukan da kake aiwatarwa ko tallafawa, hakan yana ƙarfafa ni cewa lallai kai shugaba ne nagari,” in ji shi.
A baya, Adeniyi ya ja hankalin jama’a a watan Fabrairun 2026, bayan rahotanni sun bayyana cewa ya ciwo bashi ta hanyar dandalin bayar da rance na intanet na OPay domin yi wa motarsa kwalliya da saƙonnin tallata ƙoƙarin sake zaɓen Gwamna Oyebanji.
Direban, wanda ke gudanar da aikinsa a yankin kasuwar katako ta BAO da ke kan titin Ilawe a Ado-Ekiti, ya bayyana a lokacin cewa ya ɗauki wannan mataki ne saboda irin sha’awar da yake da ita ga gwamnatin gwamnan.
Ya kuma yaba wa Oyebanji da Tinubu kan manufofinsu a fannonin ilimi, kiwon lafiya da walwalar jama’a, tare da kira ga mazauna jihar da su goyi bayan sake zaɓen gwamnan.
A cikin sabon bidiyon, Adeniyi ya ce ya sake karɓar bashi domin nuna goyon bayansa ga ’yan siyasar.
