Kamfanin man fetur na Nijeriya NNPCL ya tsawaita rangwamen Naira 66 kan kowace litar fetur har zuwa ranar 31 ga Oktoba, lamarin da zai bai wa masu ababen hawa ƙarin makonni uku na samun sauƙin kuɗin mai, a daidai lokacin da farashinsa ke ƙaruwa sakamakon rikicin gabas ta tsakiya.
Kamfanin ya ce rangwamen, wanda aka fara bayarwa a ranar 1 ga Oktoba domin bikin cika shekaru 66 da samun ƴancin kai na Nijeriya, zai ci gaba da aiki har zuwa ƙarshen watan Oktoba a dukkan gidajen mai na kamfanin da ke faɗin ƙasar, kamar yadda Jaridar Punch ta ruwaito
Tsawaita rangwamen ya biyo bayan sabbin matakan da gwamnatin Nijeriya ta ɗauka domin rage wa gidaje, ƴan kasuwa da sauran ɓangarorin tattalin arziki raɗaɗin tashin farashin ɗanyen mai a kasuwannin duniya.
A ranar Alhamis ne gwamnatin tarayya ta sanar da cewa NNPCL zai yi watsi da ribar da yake samu daga sayar da fetur a gidajen mansa, domin sayar da shi ga ƴan Nijeriya cikin rangwame, a matsayin wani mataki na rage musu tasirin hauhawar farashin ɗanyen mai a duniya.
Ministan Kuɗi kuma mai kula da tattalin arzikin ƙasa, Taiwo Oyedele, ya bayyana cewa kamfanin NNPCL zai bayar da rangwamen fetur a gidajen man sa da ke faɗin ƙasar na tsawon kwanaki 30, tare da ba wa masu harkokin sufurin jama’a fifiko.
Sai dai a cikin wata sanarwa da babban jami’in hulɗa da jama’a na kamfanin, Andy Odeh, ya fitar a ranar Juma’a, NNPC ya ce rangwamen Naira 66 kan kowace litar fetur, wanda aka fara a ranar 1 ga Oktoba, 2026, domin bikin cika shekaru 66 da samun ƴancin kai na Nijeriya, zai ci gaba har zuwa ranar 31 ga Oktoba, 2026, a dukkan gidajen man kamfanin da ke faɗin ƙasar.
Ya ce an ƙaddamar da shirin ne domin samar wa ƴan Nijeriya sauƙi a aikace, ba tare da sauya manufar gwamnati ta barin farashin man fetur ya dogara da yanayin kasuwa ba.
Kamfanin ya bayyana cewa: “Bayan sanarwar da Ministan Kuɗi kuma mai kula da tattalin arzikin ƙasa, Taiwo Oyedele, ya yi a ranar 8 ga Oktoba, 2026, NNPC Limited ya sake jaddada aniyarsa ta yin aiki tare da gwamnati da sauran masu ruwa da tsaki domin rage tasirin hauhawar farashin mai kan gidaje, ’yan kasuwa da sauran ɓangarorin tattalin arziki.
