DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Tuesday, September 15, 2026
HomeLabaraiTinubu ba shi da kwarewar magance matsalar tsaro — APM

Tinubu ba shi da kwarewar magance matsalar tsaro — APM

Jam’iyyar Allied Peoples Movement (APM) ta zargi gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu da yin fatali da gaskiyar halin da ake ciki dangane da ikirarin da take yi na cewa harkokin tsaro sun inganta a faɗin Nijeriya.

Jaridar Daily Trust ta bayyana cewa sakataren yaɗa labarai na jam’iyyar APM na ƙasa, Abubakar Yusuf, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa a ranar Asabar, inda ya soki kalaman ministan tsaro, Janar Christopher Musa (mai ritaya), wanda ya bayyana a kafar talabijin cewa yanayin tsaro ya inganta a ƙasar.

Yusuf ya bayyana cewa kalaman ministan sun nuna halin ko-in-kula da gwamnatin ke nunawa ga halin ƙuncin da ‘yan Nijeriya ke ciki, yana mai cewa rahoton ta’addanci na duniya (GTI 2026) ya nuna cewa Nijeriya ce ƙasa ta huɗu mafi muni a fannin rashin tsaro a duniya, bayan da matsayinta ya ƙara taɓarɓarewa daga lamba ta shida a shekarar 2025.

Jam’iyyar adawar ta ƙalubalanci shugaban ƙasar, ministan tsaro, da sauran manyan jami’an gwamnati da su yi tafiya a kan manyan hanyoyin ƙasar ta mota ba tare da jami’an tsaro masu ɗauke da makamai ba, domin tabbatar da ikirarin cewa tsaro ya samu.

APM ta ƙara da cewa rashin tsaro na ci gaba da ƙamari ne saboda Shugaba Tinubu ba shi da ƙwarewa da dabarun magance ƙalubalen, inda ta yi kira ga ‘yan Nijeriya da su zaɓi ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar, Gwamna Seyi Makinde, wanda ke da ingantaccen tsarin magance matsalar a zaɓen 2027.

Ukashatu Wakili
Ukashatu Wakilihttps://dclhausa.com
Ukashatu Wakili is a journalist and media professional serving as Deputy Managing Editor and Internship Coordinator at DCL Hausa. He has extensive experience in broadcast and digital journalism, with expertise in news reporting, editorial production, newsroom coordination and journalist training. He holds a B.Sc. in Mass Communication from Usmanu Danfodiyo University, Sokoto.
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata