Jam’iyyar ADC bangaren Nafi’u Gombe ta kara kaimi wajen fadada karfinta gabanin zaben 2027, inda ta yi kira ga tsohon Shugaban Nijeriya Goodluck Jonathan, tsohon Shugaban Majalisar Dattawa Bukola Saraki, da sauran manyan ’yan siyasa su shiga jam’iyyar.
Jam’iyyar ta bayyana hakan ne bayan kaddamar da Kwamitin Taron Yankin Arewa Maso Gabas, wanda ta ce wani muhimmin mataki ne na karfafa tsari a cikin gida da kuma shirya kanta don shugabanci a kasa. Shugaban jam’iyyar na tsagin, Nafiu Gombe, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa bayan taron da aka yi a Jihar Gombe ranar 11 ga Janairu.
A cikin sanarwar, ADC ta ce ta nada Patience Alex a matsayin shugabar Kwamitin Taron Yankin, yayin da Abayomi Adekunle ya zama shugaban Kwamitin Karbar Korafe-korafe. Jam’iyyar ta ce wannan mataki na nuna kudirinta na tabbatar da dimokuradiyya a cikinta da kuma gaskiya a harkokin jam’iyya.
ADC ta ce tana gayyatar manyan shugabanni irinsu Gwamnan Bauchi Bala Mohammed, Gwamnan Adamawa Ahmadu Fintiri, Gwamnan Oyo Seyi Makinde, Gwamnan Abia Alex Otti, da Shugaban Majalisar Dattawa Godswill Akpabio, tana mai cewa kwarewarsu na da muhimmanci wajen gina Nijeriya mai nagarta, hadin kai da ci-gaba mai dorewa gabanin zaben 2027.
