Mutumin da ke ikirarin shi ne Darakta Janar na Hukumar PFIPC ta bogi Adeniyi Adeyemi, ya bayyana cewa a shirye yake ya ba Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa Mai Zaman Kanta (ICPC) cikakken haɗin kai a binciken da take yi kan wannan hukuma da ake zargin ba a hukumance aka samar da ita ba.
Adeyemi ya bayyana hakan ne a ranar Talata yayin wata tattaunawa da ya yi ta kafar Instagram da fitaccen mai tasiri a kafafen sada zumunta, VeryDarkMan, ya fitar sa’o’i kaɗan bayan Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya umarci ICPC da ta binciki ayyukan wannan hukuma da ake zargin ta bogi ce.
Hakazalika, Adeyemi ya ce a shirye yake ya miƙa duk wasu takardun da ke hannunsa ga hukumomin tsaro domin taimaka wa binciken da ake ci gaba da yi kan cece-ku-cen da suka dabaibaye wannan hukuma.
