DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Wednesday, July 8, 2026
HomeKasuwanciDangote zai gina matatar mai ta dala biliyan 17 a Kenya

Dangote zai gina matatar mai ta dala biliyan 17 a Kenya

Kamfanin Dangote ya sanar da cewa yana shirin gina babbar matatar mai ta kimanin dala biliyan 17 a ƙasar Kenya, wani aiki da ake sa ran zai ƙarfafa fannin makamashi a Gabashin Afirka tare da rage dogaro da shigo da tataccen mai daga ƙasashen waje.

A cewar kamfanin, an kammala zaɓen wurin da za a gina matatar, ana ci gaba da gwajin ƙasa, yayin da aka fara ayyukan zane da ƙirar aikin. Ana sa ran matatar za ta fi samar da man fetur ga Kenya da maƙwabtan ƙasarta.

DWAfrica ta ruwaito za a gina matatar a yankin Lamu da ke gabar tekun Kenya, kuma ana sa ran za ta kasance mai kama da babbar matatar Dangote da ke Nijeriya.

Wannan shiri na daga cikin dabarun hamshaƙin attajirin ɗan kasuwar Nijeriya, Aliko Dangote, na faɗaɗa ayyukan tace mai a faɗin Afirka domin ƙarfafa tsaron makamashi da rage dogaro da shigo da tataccen mai daga ƙasashen waje.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata