Kwamitin Majalisar Dattawa mai kula da Harkokin Raya Yankunan Nijeriya ya nuna damuwa kan yadda Hukumar Raya Arewa maso Yamma (NWDC) ke kashe kuɗaɗenta.
A yayin zaman binciken, sanatoci sun ce daga cikin Naira biliyan 1.19 da hukumar ta kashe, kusan Naira miliyan 943, wato kusan kashi 79 cikin 100, an kashe su ne wajen alawus-alawus na mambobin kwamitin gudanarwa.
Gidan talabijin na NTA ya ruwaito cewa kwamitin ya kuma tambayi dalilin da ya sa NWDC ce kaɗai daga cikin hukumomin raya yankuna da ba ta da manyan daraktoci da ma’aikata tun bayan ƙaddamar da ita a watan Fabrairun 2025.
Sai dai ma’aikatar da ke sa ido kan hukumar, tare da shugabannin hukumar da Manajan Darakta, sun bayyana wa kwamitin wasu matsalolin da suka ce suna hana gudanar da ayyukanta yadda ya kamata.
Kwamitin ya jaddada cewa akwai buƙatar ɗaukar matakan gaggawa domin hukumar ta cimma manufarta ta bunƙasa ci gaba da inganta tsaro a yankin Arewa maso Yamma.
