DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Jami’an tsaron Chadi hudu sun kwanta dama a wata fafatawa da wasu mahara a arewacin kasar

-

Lamarin ya faru ne da yammacin ranar 17, ga watan Febarairun da muke ciki a lokacin da wata motar jigilar wani kamfani ke cikin tafiya kan hanyar da ke tsakanin Faya da Kouba Olanga ta fada tarkon wasu mutane masu dauke makamai inda nan take suka halaka direban motar.

To sai dai rahotanni na nuni da cewa kwana daya bayan hallaka direban ne wasu makusanta shi suka farwa maharan da suka halakashi, nan ne jami’an tsaro suka shiga lamarin, a yayin fafatawar su da maharan manyan jami’an tsaron Chadin hudu suka kwanta dama, sai dai a cewar majiyar tsaro su ma maharan an hallaka uku daga cikin su.

Google search engine

Wata majiya daga gwamnatin kasar ta ce za a kara tsaurara tsaro nan gaba a yankin da ke cikin hamada sahara wanda yake fama da hare hare a kan hanya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Masu zanga zanga a SĂ©nĂ©gal na neman adalci ga dalibin Jami’ar Cheikh Anta Diop ta birnin Dakar da aka halaka

Masu zanga zangar da suka hada da magoya bayan jam'iyya mai mulki ta Pastef sun amsa kiran wata hadaka ce ta dalibai da 'yan fafutikar...

Shugaba Tinubu ya taya waɗanda suka samu nasara a zaɓukan Abuja, Kano da Rivers, murna

Shugaba Tinubu ya taya waɗanda suka samu nasara a zaɓen ƙananan hukumomin Abuja da kuma zaɓen cike gurbi da aka gudanar a jihohin Kano da...

Mafi Shahara