Mahukunta a Burtaniya sun sanar da tsauraran matakan tsaro a garin Windsor yayin da Shugaban Nijeriya, Bola Ahmed Tinubu, zai kai ziyara ta musamman a mako mai zuwa bisa gayyatar Sarkin Birtaniya, King Charles III.
‘Yan sandan Thames Valley sun ce za a kara takaita zirga-zirgar jiragen sama a sararin samaniyar Windsor daga karfe 7 na safe zuwa karfe 11:59 na dare a ranar 18 ga Maris, yayin da za a tura jami’an tsaro da suka hada da masu makamai, rundunar doki da jami’an kula da hanyoyi.
Hukumomin sun ce za a kuma yi amfani da na’urorin CCTV, katangar tsaro da sauran matakai domin tabbatar da tsaron ziyarar da za a yi a Windsor Castle, tare da gargadin cewa duk wanda ya karya dokar hana zirga-zirgar jiragen sama zai fuskanci hukunci.



