Hukumar da ke lura da tashoshin jiragen ruwa ta Nijeriya (NPA) ta bayyana cewa jiragen ruwa guda 19 na ci gaba da sauke kayayyakin man fetur da sauran hajojin kasuwanci a tashoshin jiragen ruwa na Legas.
Jaridar Daily Nigerian ta ruwaito hukumar ta bayyana hakan ne cikin rahotonta na yau da kullum mai taken Shipping Position, wanda ta fitar ga manema labarai a ranar Asabar, inda ta ce ana ci gaba da gudanar da ayyukan sauke kaya domin bunkasa harkokin kasuwanci da samar da kayayyaki a ƙasar.
