Shugaban ma’aikatan fadar shugaban ƙasa, Femi Gbajabiamila, ya bayyana cewa bai taɓa cin amanar da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ɗora masa ba, yana mai jaddada cewa bincike ya wanke shi daga zarge-zargen da aka dinga yi masa a ‘yan watannin nan.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa Gbajabiamila ya bayyana hakan ne a ranar Asabar a birnin Legas, yayin bikin raba kayan tallafi na shekarar 2026 da aka gudanar a babban filin wasa na ƙasa da ke Surulere.
Zarge-zargen da aka yi masa sun samo asali ne daga binciken da aka gudanar kan wata bogin hukuma mai suna Presidential Foreign Intervention Promotion Council (PFIPC), inda aka yi zargin yana da hannu a harkokinta. Sai dai binciken da hukumomi daban-daban suka gudanar, ciki har da wanda Majalisar Wakilai ta yi, ya wanke tsohon Kakakin Majalisar daga dukkan zarge-zargen.
Gbajabiamila ya bayyana cewa an bi tsarin doka wajen gudanar da binciken, duk da matsin lambar da wasu ɓangarori suka yi na ganin an yanke masa hukunci kafin a kammala bincike.
Ya ce, “Watannin da suka gabata an jarrabe ni ta hanyoyin da ban taɓa tsammani ba. An rubuta labarai daban-daban, an yi zarge-zarge marasa tushe, an yi ƙarairayi, kuma an nemi ɓata mutuncina. Sakamakon binciken a bayyane yake ga kowa. Shugaban Ƙasa ya san shugaban ma’aikatansa sosai. Da yake ya daɗe yana aiki tare da ni, ya kasance mai cikakken yaƙinin cewa ba ni da wata alaƙa da waɗancan miyagun abubuwa.”
Ya ƙara da cewa babu wani adadi na maƙudan kuɗi, baƙar magana, ko ƙarairayi da za su janye hankalinsa daga sauke nauyin da shugaban ƙasa ya ɗora masa a fadar gwamnati.
Da yake magana kan alaƙarsa da Tinubu, Gbajabiamila ya jaddada cewa biyayyarsa ga shugaban ƙasar na nan daram. “A harkar siyasa, biyayya ita ce babban ginshiƙi. Na daɗe tare da Mai Girma Shugaban Ƙasa… Ban taɓa nuna shakku kan jagorancinsa ba kuma ban taɓa cin amanarsa ba. Na kasance mai biyayya a baya kuma har yanzu ina nan a kan hakan,” in ji shi.
A wurin taron, Mataimakin Gwamnan Jihar Legas, Dokta Obafemi Hamzat, ya yaba wa Gbajabiamila kan yadda yake ci gaba da taimaka wa al’umma, inda aka raba kuɗaɗe, motoci, babura masu ƙafa uku masu amfani da wutar lantarki, motocin bas, motocin sintirin tsaro, da motar asibiti ga mutane kusan 5,000.
