Majalisar Dattawan Nijeriya ta bai wa kamfanin mai na Nijeriya NNPCL wa’adin zuwa ranar 29 ga watan Afrilun 2026, domin ya yi cikakken bayani kan wasu tambayoyin bincike da suka shafi kuɗaɗe da suka kai kusan Naira tiriliyan 210.
Wannan mataki ya biyo bayan rashin gamsuwar da Majalisar Dattawan Nijeriya ta nuna kan bayanan da kamfanin ya gabatar dangane da rahotannin bincike na shekaru da dama, musamman daga 2017 zuwa 2023.
Sanatocin sun bayyana cewa amsoshin da aka kawo ba su wadatar ba, kuma sun ƙunshi gibi da dama.
Kwamitin majalisar mai kula da asusun gwamnati ne ya jagoranci wannan bincike, inda ya bukaci shugabannin kamfanin na yanzu da na baya su halarci zaman bincike domin su yi karin haske.
An jaddada cewa dole ne duk masu ruwa da tsaki su bayyana gaskiya kan yadda aka tafiyar da waɗannan kuɗaɗe masu yawa.
Daga cikin batutuwan da ke jawo hankali akwai wasu kuɗaɗe da suka haura Naira tiriliyan 100 da aka bayyana a matsayin basussuka, amma ba a yi cikakken bayani kan yadda aka tara su ko yadda za a biya su ba.
Haka kuma akwai wasu makudan kuɗaɗe da aka danganta da ayyukan haɗin gwiwa (joint ventures) da ba a fayyace yadda aka sarrafa su ba.
Shugaban kwamitin, Sanata Aliyu Wadada, ya nuna damuwa kan yadda aka tafiyar da harkokin kuɗi a kamfanin, yana mai cewa al’ummar Nijeriya na da cikakken ‘yancin sanin yadda ake sarrafa dukiyar ƙasa.
Wasu daga cikin sanatocin sun kuma koka kan yadda jami’an kamfanin NNPCL ke yawan jinkirtawa ko ƙin amsa gayyatar majalisar a baya, abin da suka ce na kawo tsaiko ga aikin sa ido da majalisa ke yi kan harkokin gwamnati.
Majalisar ta yi gargadi cewa idan har kamfanin bai gabatar da gamsassun bayanai kafin cikar wa’adin ba, za a ɗauki matakan doka domin tilasta masa yin hakan.
