DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Thursday, April 16, 2026
HomeWasanniArbeloa na iya barin aikin horas da Real Madrid bayan kakar wasan...

Arbeloa na iya barin aikin horas da Real Madrid bayan kakar wasan bana

Tsohon ɗan wasan ƙungiyar Real Madrid, Álvaro Arbeloa, na shirin barin aikinsa na horaswa a ƙarshen kakar wasa ta bana, kamar yadda rahoton The Athletic ya bayyana.

Rahoton ya nuna cewa Arbeloa, na duba yiwuwar ajiye aikinsa bayan kammala kakar wasan, matakin da ya jawo cece-kuce a tsakanin magoya bayan kungiyar.

Ko da yake ba a bayyana cikakken dalilin da ya sa yake son barin mukamin nasa ba, ana hasashen cewa matakin na iya kasancewa mai nasaba da sauye-sauyen da ake shirin aiwatarwa a cikin tsarin ƙungiyar, musamman a ɓangaren horas da ‘yan wasa.

Álvaro Arbeloa ya kasance daga cikin fitattun ‘yan wasan Real Madrid a lokacin da yake taka leda, inda ya taka muhimmiyar rawa a nasarorin da ƙungiyar ta samu a cikin gida da nahiyar Turai.

A lokacin da yake taka leda, Arbeloa ya taimaka wa ƙungiyar lashe manyan kofuna, ciki har da gasar UEFA Champions League da kuma gasar La Liga, inda ya nuna ƙwarewa a matsayin mai tsaron baya.

Bayan yin ritaya daga taka leda, Arbeloa ya koma fannin horaswa, inda ya fara aiki da ƙananan ‘yan wasa a tsarin matasa na Real Madrid.

Har yanzu babu wata sanarwa a hukumance daga Real Madrid ko daga Arbeloa kansa dangane da wannan batu, lamarin da ke nuna cewa ana ci gaba da sa ido kan yadda al’amura za su kasance a nan gaba.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata