Mai ba Shugaba Tinubu shawara kan harkokin yaɗa labarai, Bayo Onanuga, ya caccaki tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, kan kalaman da ya yi game da batun rabon mulki tsakanin Arewa da Kudu (zoning) gabanin zaɓen 2027.
Onanuga ya bayyana cewa Atiku “ba zai taɓa koyo ba,” yana mai zarginsa da ƙoƙarin karya tsarin rabon mulki da aka saba amfani da shi a siyasar Nijeriya.
Ya ce a ganinsa, ya kamata Bola Ahmed Tinubu ya kammala wa’adinsa na shekaru takwas, kamar yadda tsohon shugaba Muhammadu Buhari ya yi.
A cewarsa, yankin Kudu ne ke da damar ci gaba da riƙe mulki har zuwa shekarar 2031, don haka ya buƙaci Atiku da ya hakura da tunanin sake tsayawa takarar shugaban ƙasa a 2027.
Ya kuma zargi tsohon mataimakin shugaban da gabatar da hujjoji masu son rai domin cimma burinsa na siyasa.
Wannan martani na Onanuga ya biyo bayan wata hira da Atiku ya yi, inda ya bayyana cewa babu wata yarjejeniya ta ƙasa baki ɗaya da ta wajabta rabon mulki tsakanin Arewa da Kudu.
Duk da haka, ya ce yana goyon bayan tsarin, amma ya jaddada cewa shi tsarin jam’iyyu ne, musamman a cikin jam’iyyar PDP.
Sai dai Onanuga ya yi watsi da wannan ƙididdiga, yana mai cewa rashin daidaito da ya faru a baya ya samo asali ne daga rasuwar marigayi shugaban ƙasa Umaru Musa Yar’Adua, wanda hakan ya bai wa Goodluck Jonathan damar karɓar mulki.
Wannan batu nasa ya ƙara tayar da kura a fagen siyasar Nijeriya, musamman yayin da ake shirin tunkarar zaɓen 2027.
