DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Thursday, April 16, 2026
HomeSiyasaTinubu ya taya Wadagni murnar lashe zaben shugaban kasar Benin

Tinubu ya taya Wadagni murnar lashe zaben shugaban kasar Benin

Shugaban Nijeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya taya zaɓaɓɓen shugaban ƙasar Benin, Romuald Wadagni murnar samun nasara a zaɓen shugaban ƙasa da aka gudanar a ranar 12 ga watan Afrilu, 2026.

Tinubu ya bayyana wannan taya murna ne a cikin wata wasiƙa da ya sanya wa hannu da kansa, inda ya yaba da yadda aka gudanar da zaɓen cikin lumana da kwanciyar hankali.

Romuald Wadagni, wanda a baya yake riƙe da muƙamin Ministan Kuɗi na ƙasar Benin, ya samu gagarumar nasara a zaɓen, abin da ke nuna irin goyon bayan da jama’ar ƙasar suka ba shi.

Shugaba Tinubu ya ce wannan nasara wata alama ce ta amincewa da hangen nesan Wadagni da kuma irin ƙwarewar da ya nuna a lokacin da yake jagorantar harkokin kuɗin ƙasar.

A cikin wasiƙar tasa, Tinubu ya jaddada cewa Nijeriya da Benin suna da tsohuwar alaƙar zumunci da haɗin kai, wadda ta haɗa da al’adu, kasuwanci da kuma hulɗar siyasa.

Ya ce yana fatan yin aiki kafaɗa da kafaɗa da sabon shugaban domin ƙarfafa wannan dangantaka da kuma bunƙasa ci gaban yankin.

Haka kuma, Shugaban na Nijeriya ya yaba wa al’ummar Benin bisa jajircewarsu wajen tabbatar da tsarin dimokuraɗiyya da zaman lafiya a lokacin zaɓen.

Ya bayyana cewa wannan sauyin mulki wata muhimmiyar alama ce a tarihin ƙasar, wadda ke nuna yadda al’umma ke mutunta tsarin zaɓe da zaman lafiya.

Tinubu ya kuma nuna cewa haɗin gwiwar da ke tsakanin ƙasashen biyu zai taimaka wajen ƙarfafa tsaro a yankin ECOWAS da kuma bunƙasa tattalin arziki a nahiyar Afirka baki ɗaya.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata