DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Wednesday, May 13, 2026
HomeLabaraiMasu neman gwamna sun ƙalubalanci tsarin sulhu a APC ta Yobe

Masu neman gwamna sun ƙalubalanci tsarin sulhu a APC ta Yobe

Masu neman takarar gwamnan Jihar Yobe guda shida a ƙarƙashin jam’iyyar APC sun yi watsi da zaɓen tsohon Sakataren Gwamnatin Jihar, Alhaji Baba Mallam Wali, a matsayin ɗan takarar sasanci na jam’iyyar a zaɓen 2027.

’Yan takarar sun bayyana cewa za su amince ne kawai da sahihin zaɓen fidda gwani mai gaskiya da adalci domin zaɓen ɗan takarar gwamna.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa masu neman takarar sun haɗa da Sanata Ibrahim Mohammed Bomai, Bashir Sheriff Machina, Kashim Musa Tumsah, Injiniya Mustapha Yunusa Maihaja, Lawan Kolo Geidam da tsohon Sufeto Janar na ’Yan Sanda, Usman Alkali Baba.

A wata sanarwa bayan taronsu a Abuja, sun ce zaɓen Baba Mallam Wali ya saɓa wa dokar zaɓe da kundin tsarin APC.

Sun jaddada cewa idan za a yi tsarin sulhu, dole ne a bi dukkan tanade-tanaden doka da kundin tsarin jam’iyyar.

Masu neman takarar sun kuma bayyana rashin amincewa da shugaban APC na jihar, Alhaji Mohammed Gadaka, suna zarginsa da nuna son kai a tsarin siyasar da ake gudanarwa.

Saboda haka suka buƙaci a cire shi daga duk wani aiki da ya shafi gudanarwa da sa ido kan zaɓen fidda gwani na gwamna a jihar.

Sai dai sun sake bayyana goyon bayansu ga shugabancin APC na ƙasa tare da marawa Shugaba Bola Ahmed Tinubu baya kan sake tsayawa takara.

Rahotanni sun ce wasu masu ruwa da tsaki a siyasar Yobe ne suka amince da Baba Mallam Wali a matsayin wanda ake so ya gaji Gwamna Mai Mala Buni bayan wa’adinsa ya ƙare a 2027.

Ukashatu Ibrahim Wakili
Ukashatu Ibrahim Wakilihttps://dclhausa.com
Ukashatu Wakili, Mataimakin Manajan Edita kuma Mai Kula da Shirin Koyon Sanin Makamar Aiki ne a DCL Hausa. A matsayinsa na ƙwararren ɗan jarida yana tsara ayyukan rediyo da kafafen sada zumunta, fassarar labarai, da tabbatar da sahihancin bayanai. Yana jagorantar shirin horaswa ga masu koyon aiki tare da kula da ingancin rubuce-rubuce da shirye-shiryen gidan jaridar.
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata