DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Wednesday, May 13, 2026
HomeLabarai'Har yanzu Hope Uzodimma ne shugaban ƙungiyar gwamnonin APC'

‘Har yanzu Hope Uzodimma ne shugaban ƙungiyar gwamnonin APC’

Kungiyar gwamnonin APC ta PGF ta musanta rahotannin da ke cewa an cire gwamnan Jihar Imo, Hope Uzodimma, daga shugabancin ƙungiyar.

A wata sanarwa da Darakta Janar na ƙungiyar, Folorusho Aluko, ya fitar ranar Laraba, PGF ta bayyana rahotannin a matsayin ƙarya da marasa tushe.

Gidan talabijin na Channels ya ruwaito cewa ƙungiyar ta ce ba a gudanar da wani taro da aka yanke hukuncin cire Uzodimma daga mukaminsa ba.

Sanarwar ta ƙara da cewa sakatariyar PGF ba ta da wani bayani ko matsaya da ta shafi cire shugaban ƙungiyar daga muƙaminsa.

Kungiyar ta ce har yanzu tana haɗe kai kuma tana ci gaba da gudanar da ayyukanta yadda ya kamata.

PGF ta kuma buƙaci jama’a da magoya bayan APC da kafafen yaɗa labarai su yi watsi da rahotannin, tana mai jaddada cewa Gwamna Hope Uzodimma na ci gaba da samun goyon bayan gwamnonin APC.

Ukashatu Ibrahim Wakili
Ukashatu Ibrahim Wakilihttps://dclhausa.com
Ukashatu Wakili, Mataimakin Manajan Edita kuma Mai Kula da Shirin Koyon Sanin Makamar Aiki ne a DCL Hausa. A matsayinsa na ƙwararren ɗan jarida yana tsara ayyukan rediyo da kafafen sada zumunta, fassarar labarai, da tabbatar da sahihancin bayanai. Yana jagorantar shirin horaswa ga masu koyon aiki tare da kula da ingancin rubuce-rubuce da shirye-shiryen gidan jaridar.
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata