DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Thursday, May 14, 2026
HomeSiyasaGwamnan Bauchi Bala Muhammad zai yi takarar sanata a jam'iyyar APM

Gwamnan Bauchi Bala Muhammad zai yi takarar sanata a jam’iyyar APM

Gwamnan Jihar Bauchi, Bala Mohammed, ya sayi fom ɗin tsayawa takara da na nuna sha’awa domin neman kujerar Sanatan Bauchi ta Kudu a ƙarƙashin jam’iyyar Allied Peoples Movement (APM).

Gwamnan ya bayyana hakan ne jim kaɗan bayan dawowarsa daga Abuja, inda ya halarci taron kwamitin zartarwa na ƙasa (NEC) na jam’iyyar a ranar Alhamis.

A wani ci gaba na daban kuma, Sanatan da ke wakiltar mazabar Bauchi ta Tsakiya, Abdul Ahmed Ningi, ya sanar da ficewarsa daga jam’iyyar PDP

Ningi ya bayyana hakan ne cikin wata wasiƙar murabus da ya aike wa shugaban PDP na mazabar Ningi a karamar hukumar Ningi ta Jihar Bauchi.

Sanatan, wanda ya shafe sama da shekaru 20 yana cikin PDP, ya ce ya ɗauki wannan mataki ne sakamakon rikicin cikin gida da ya dade yana addabar jam’iyyar.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata