DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Thursday, May 14, 2026
HomeLabaraiNijeriya da Amurka za su karfafa hadin gwiwa kan matsalar tsaro

Nijeriya da Amurka za su karfafa hadin gwiwa kan matsalar tsaro

Mai ba shugaban Nijeriya shawara kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu, ya gana da manyan jami’an gwamnatin Amurka kan haɗin gwiwar tsaro don yaki da ta’addanci a kasar.

Ribadu ya kai ziyarar aiki ta kwanaki uku a Amurka daga ranar 4 zuwa 6 ga watan Mayu, inda ya gana da mataimakin shugaban ƙasa J. D. Vance da kuma sakataren harkokin waje Marco Rubio, wanda kuma ke riƙe da muƙamin mai ba da shawara kan tsaron ƙasa na riƙo.

Haka kuma ya gana da mataimakiyar sakatare mai kula da harkokin siyasa Allison Hooker da mataimakin sakatare a ma’aikatar yaƙi Daniel Zimmerim a yayin ziyarar, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.

A cikin wata sanarwa da mai ba shugaban Tinubu shawara kan yaɗa labarai, Bayo Onanuga, ya fitar a ranar Asabar, ya ce Ribadu ya isar da ƙudurin shugaban ƙasa na ƙarfafa dangantakar ƙasashen biyu yayin ganawar.

Bangarorin biyu sun duba halin da dangantakar Nijeriya da Amurka ke ciki a yanzu, tare da tattauna hanyoyin ƙarfafa haɗin gwiwa a fannoni kamar yaƙi da ta’addanci, musayar bayanan sirri, haɗin gwiwar tsaro, ƙarfafa tattalin arziki, da kuma inganta dimokuraɗiyya.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata