Babban Sakataren Fadar Shugaban Nijeriya, Femi Gbajabiamila, ya bayyana cewa goyon bayan da ya ke bai wa dan majalisar dokokin jihar Legas, Desmond Elliot, ya kusa janyo masa rasa mukaminsa a gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu.
Gbajabiamila ya bayyana haka ne a wani bidiyo da ya karade kafafen sada zumunta, inda ya ce Shugaba Tinubu ya taba kiran sa zuwa gidansa da ke Abuja yayin rikicin shugabancin majalisar dokokin Legas.
A cewarsa, shugaban kasar ya tambaye shi ko Desmond Elliot na daga cikin ‘yan majalisar da suka goyi bayan tsige tsohon kakakin majalisar, Mudashiru Obasa.
Ya ce nan take ya musanta cewa Elliot na cikin wadanda suka shirya tsige Obasa, yana mai cewa bai ma taba magana da shi kan lamarin ba.
Sai dai ya ce Shugaba Tinubu ya dage cewa bayanan sirri da ke hannun sa sun nuna Elliot na cikin wadanda suka haddasa rikicin.
Gbajabiamila ya ce daga baya ya kira Desmond Elliot domin sanar da shi gargadin da shugaban Tinubu ya bayar tare da bukatar ya nisanta kansa daga rikicin.
Ya kuma bayyana cewa bayan kwanaki uku, Darakta Janar na DSS ya tuntube shi yana zarginsa da hannu wajen tallafawa Elliot a rikicin majalisar Legas.
A cewarsa, ya sake musanta zargin sannan ya sake tuntubar Elliot tare da shawartar sa ya fito fili ya karyata alakanta shi da rikicin.
Rahotanni sun ce rikicin ya samo asali ne daga tsige da kuma mayar da Mudashiru Obasa kan kujerar kakakin majalisar dokokin Legas, lamarin da ya haddasa rabuwar kai a APC ta jihar.
Desmond Elliot, wanda ke wakiltar Surulere a majalisar dokokin Legas, na fuskantar kalubale wajen sake samun tikitin takara, yayin da wasu jiga-jigan APC ke adawa da neman wa’adin sa karo na hudu kamar yadda Premium Times ta ruwaito.
