DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Friday, May 15, 2026
HomeLabaraiGwamnatinmu ta janyo zuba hannun jari na kusan Dala miliyan 20 -...

Gwamnatinmu ta janyo zuba hannun jari na kusan Dala miliyan 20 – Shugaba Tinubu

Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu ya bayyana cewa Nijeriya ta samu kusan dala biliyan 20 na jarin kasashen waje a bana sakamakon sauye-sauyen tattalin arziki da gwamnatin sa ta aiwatar.

Tinubu ya bayyana haka ne yayin taron Africa CEO Forum da ke gudana a kasar Rwanda, inda ya ce manufofin gwamnatinsa sun taimaka wajen kara gaskiya, inganci da kuma karfafa gwiwar masu zuba jari a Nijeriya.

Ya ce gwamnatinsa ta mayar da Nijeriya farfajiyar harkokin kasuwanci da zuba jari, yana mai cewa hakan ne ya sa masu zuba jari daga kasashen duniya suka fara nuna sha’awa sosai.

“Ina farin cikin bayyana cewa Nijeriya ta jawo kusan dala biliyan 20 na jarin kai tsaye saboda mun samar da tsarin gaskiya, inganci da kuma bude kofar kasuwanci,” in ji Tinubu.

Shugaban kasar ya kuma bayyana cewa gwamnatinsa ba za ta ci gaba da barin fitar da albarkatun kasa ba tare da an sarrafa su a cikin gida ba.

A cewarsa, Nijeriya na da damar amfani da ma’adananta wajen samar da batirin motocin lantarki da sauran kayayyakin zamani maimakon sayar da albarkatun kasa kawai.

Tinubu ya ce gwamnati za ta cigaba da samar da yanayi mai kyau ga bangarori masu zaman kansu domin kawo jari da kwarewa wajen bunkasa masana’antu a Afirka.

Ya kuma yi kira ga kasashen Afirka su fara aiwatar da yarjejeniyar cinikayya ta AfCFTA yadda ya kamata domin bunkasa kasuwanci tsakanin kasashen nahiyar.

“Afrika ba za ta ci gaba da magana kawai ba tare da aiki ba. Dole ne mu hada kai mu yi amfani da albarkatun mu yadda ya kamata,” in ji shi.

Tinubu ya bukaci kasashen Afirka su daina dogaro da dala wajen kasuwanci tsakanin su, yana mai cewa hakan na kara tsadar kasuwanci da rashin daidaito a tattalin arziki.

A cewarsa, idan ana kera abubuwa a Nijeriya, ya kamata a rika cinikayya da naira maimakon amfani da kudaden kasashen waje.

Shugaban kasar ya kuma yaba da aikin matatar Dangote, yana mai cewa hakan ya nuna cewa Afirka na da ikon gudanar da manyan ayyukan masana’antu idan aka samar da goyon bayan gwamnati.

Ya ce, yanzu haka Nijeriya ta koma kasar da ke fitar da man fetur, man jiragen sama da sauran kayayyakin man fetur zuwa wasu kasashe.

Tinubu ya kuma yi kira da a samar da cibiyar tantance darajar kasashen Afirka saboda cibiyoyin kasashen waje ba sa fahimtar yadda tattalin arzikin Afirka ke tafiya.

Hakazalika, ya kara da cewa gwamnatin Nijeriya na shimfida kilomita 19,000 na fibre optic domin bunkasa intanet, ilimi da kasuwancin zamani a fadin kasar.

A karshe, shugaba Tinubu ya ce lokaci ya yi da kasashen Afirka za su hada kai wurin tinkarar matsalolin tattalin arziki da siyasa, yana mai cewa “Pan-Africanism ba magana kadai ba ce, dole ne a aiwatar da ita.”

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata