DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Wednesday, May 13, 2026
HomeSiyasaKwankwaso da Obi sun bukaci mu ba su tikitin takarar shugaban kasa...

Kwankwaso da Obi sun bukaci mu ba su tikitin takarar shugaban kasa a PRP, muka hana su – Hakeem Baba Ahmad

Shugaban jam’iyyar PRP na kasa, Hakeem Baba Ahmed, ya bayyana dalilin da ya sa tsohon dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour Party, Peter Obi da jagoran darikar Kwankwasiyya, Rabiu Musa Kwankwaso suka kasa shiga jam’iyyar PRP gabanin zaben 2027.

Dr Hakeem Baba Ahmed ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawar siyasa ta Hausa a gidan talabijin na DITV Kaduna da jaridar Daily Trust ta bibiya, inda ya ce tattaunawar hadin gwiwa tsakanin PRP da bangarorin ‘yan siyasar biyu ta tsaya ne bayan rashin jituwa kan sharudan shiga jam’iyyar.

A cewarsa, Obi da Kwankwaso sun tuntubi PRP domin yiwuwar hadaka, har ma aka kai matakin samar da kwamitin da zai ci gaba da tattaunawa. Sai dai ya ce daga baya bangarorin biyu sun gabatar da wasu bukatu da suka janyo sabani.

Shugaban PRP din ya ce daya daga cikin manyan matsalolin shi ne bukatar da aka gabatar na cewa tun kafin shiga jam’iyyar, a tabbatar musu da tikitin takarar shugaban kasa ba tare da wata hamayya ta cikin gida ba.

Hakeem Baba Ahmed ya ce jam’iyyar PRP ta yi watsi da wannan bukata, tana mai cewa tsarin jam’iyyar bai amince da ba da tikiti kai tsaye ba tare da bin dokoki da tsarin dimokuradiyya na cikin gida ba.

Ya kara da cewa duk da PRP ta amince cewa Obi da Kwankwaso manyan ‘yan siyasa ne masu karfi da magoya baya, amma jam’iyyar ba za ta karya kundinta domin amfanin wani mutum ba.

Haka kuma, ya bayyana cewa bangarorin ‘yan siyasar biyu sun bukaci a ba su wasu muhimman mukamai a cikin jam’iyyar saboda yawan magoya bayan da suke son kawowa PRP.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata