Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu ya bukaci shugabanni da mambobin jam’iyyar APC su hada kai tare da kauce wa rikici yayin gudanar da zaben fidda gwani na jam’iyyar domin tunkarar zaben 2027.
Tinubu ya bayyana haka ne a wata sanarwa da ya sanya wa hannu da kansa, inda ya ce APC na shirin shiga zagaye na hudu na zabuka tun bayan kafuwar jam’iyyar.
Ya ce jam’iyyar APC an gina ta ne bisa turbar siyasar ci gaba, hadin kai da sadaukarwa, yana mai cewa dole ne a ci gaba da kare wadannan manufofi yayin gudanar da zabukan fidda gwani.
Shugaban kasar ya bayyana cewa zaben fidda gwani da zai fara daga ranar Juma’a da na ‘yan takarar majalisar wakilai, zuwa zaben fidda gwani na shugaban kasa ranar 25 ga watan Mayu, ba kawai neman ‘yan takara ba ne, illa wata hanya ta nuna karfin hadin kan jam’iyyar.
Tinubu ya yaba da kokarin shugabannin APC wajen samar da ‘yan takarar hadaka ta hanyar maslaha, yana mai cewa hakan na rage rikici da sabani tsakanin mambobin jam’iyyar.
Sai dai ya ce idan ba a cimma matsaya ba, dole ne a gudanar da zabe cikin lumana tare da daukar juna a matsayin ‘yan uwa.
“Ba za mu amince da rikici ko siyasar gaba da gaba ba. A kowanne zabe akwai mai nasara da wanda bai yi nasara ba,” in ji Tinubu.
Ya bukaci wadanda suka yi nasara kada su yi nuna isa, yayin da wadanda suka fadi kuma su rungumi kaddara tare da shirin wata dama ta gaba.
Tinubu ya kuma gargadi shugabannin jam’iyyar da gwamnoni su tabbatar da adalci da bai wa dukkan masu neman takara dama iri daya ba tare da nuna son kai ba.
Haka kuma ya bukaci a bai wa mata da matasa kulawa ta musamman a yayin zabukan fidda gwani na jam’iyyar.
Shugaban kasar ya kuma gargadi jami’an tsaro da su kasance masu kwarewa tare da kauce wa tsoma baki wajen gudanar da zabukan fidda gwani.
