DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Friday, May 15, 2026
HomeKasuwanciDuk tsadar mai, amfani da fetur ya karu zuwa lita miliyan 52.4...

Duk tsadar mai, amfani da fetur ya karu zuwa lita miliyan 52.4 a Nijeriya

Yawan fetur da ake amfani da shi kullum a Nijeriya ya karu da kaso 10.78 cikin 100 a watan Afrilu na 2026, inda ya kai lita miliyan 52.4 duk da tashin farashin mai a duniya.

Sabbin alkaluman da Hukumar NMDPRA ta fitar sun nuna cewa an samu karin ne daga lita miliyan 47.3 da aka samu a watan Maris. Wannan na zuwa ne yayin da rikicin Gabas ta Tsakiya ya sa farashin danyen mai ya haura dala 106 kan kowace ganga zuwa ranar Laraba.

Rahotanni sun ce rufe mashigar ruwa ta Hormuz da Iran ke iko da ita ya haddasa tangardar jigilar danyen mai da tankokin fetur, lamarin da ya kara dagula kasuwar makamashi a duniya.

Bayanai sun ce matatun mai na cikin gida ciki har da matatar Dangote na fuskantar matsalar samun danyen mai, domin har yanzu suna dogaro sosai kan shigo da shi daga kasashen waje, inda farashinsa ke sauyawa bisa yanayin kasuwar duniya.

Tun bayan barkewar yakin Iran da Isra’ila da Amurka a watan Fabrairu, farashin fetur ya yi tashin gwauron zabi a Nijeriya, inda matsakaicin farashin kowace lita ya kai kusan Naira 1,370 a watan Afrilu, idan aka kwatanta da N1,180 da aka samu a watan Maris.

Sai dai duk da wannan karin farashi da ya kai kusan kaso 13.8 cikin 100, bayanan NMDPRA sun nuna cewa yawan amfani da fetur ya ci gaba da karuwa a watan Afrilu.

Rahoton watan Afrilu na 2026 ya nuna cewa hadadden yawan fetur da matatar Dangote da kuma shigo da kaya daga kasashen waje suka samar ya karu da kaso 10.7 cikin 100, inda ya kai lita miliyan 44.4 a rana idan aka kwatanta da lita miliyan 40.1 a watan Maris.

Binciken alkaluman ya nuna cewa samar da fetur daga matatar Dangote ya karu da kaso 19 cikin 100 zuwa lita miliyan 40.7 a rana daga lita miliyan 34.2 a watan Maris. A gefe guda kuma, shigo da fetur daga waje ya ragu da kaso 37.3 cikin 100 zuwa lita miliyan 3.7 daga lita miliyan 5.9.

Rahoton ya kuma nuna cewa shigo da danyen mai daga kasashen waje ya ragu da kaso 95.65 cikin 100 zuwa ganga miliyan 0.41 a watan Afrilu daga ganga miliyan 9.43 a watan Maris.

Hakazalika, samar da danyen mai daga kamfanonin hako mai na cikin gida zuwa matatun cikin ƙasa ya karu da kaso 56 cikin 100, inda ya kai ganga miliyan 17.99 a watan Afrilu idan aka kwatanta da ganga miliyan 11.48 a watan Maris.

A cewar NMDPRA, matatar Dangote mai ƙarfin tace ganga dubu 650,000 a rana ta kai matakin aiki na kaso 99.12 cikin 100 a watan Afrilu, yayin da matatun gwamnati na Fatakwal, Warri da Kaduna suka ci gaba da zama babu aiki.

Rahoton ya kuma bayyana cewa yawan danyen man da Nijeriya ke hakowa ya karu kadan zuwa ganga miliyan 1.663 a rana a watan Afrilu daga ganga miliyan 1.546 a watan Maris, ciki har da condensates.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata