Shugaban Amurka Donald Trump da shugaban kasar China Xi Jinping sun tattauna kan mashigar ruwa ta Hormuz yayin wata ganawa da suka yi a Beijing, inda fadar White House ta ce Xi ya amince cewa dole ne mashigar ta cigaba da kasancewa a bude domin tabbatar da zirga-zirgar makamashi cikin sauki yayin da rikicin Iran ke ci gaba da girgiza kasuwannin duniya.
A lokaci guda kuma, ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi ya bukaci kasashen kungiyar BRICS su yi Allah wadai da yakin da Amurka da Isra’ila ke yi da Iran, yana mai cewa kasarsa ba za ta taba mika wuya ga matsin lamba ba.
Araghchi ya bayyana hakan ne yayin taron BRICS+ da aka gudanar a birnin New Delhi na kasar India, inda ya zargi Amurka da Isra’ila da karya dokokin kasa da kasa ta hanyar kai hare-hare kan Iran.
Aljazeera ta ruwaito cewa, Ministan ya kuma zargi Hadaddiyar Daular Larabawa da taka rawa a yakin da ake yi da Iran, yana mai cewa kasar UAE na taimakawa wajen kai wa Tehran hari.
Rahotanni daga Iran sun ce fiye da jiragen ruwa 30, ciki har da wasu masu alaka da kamfanonin China, sun ratsa mashigar Hormuz bayan Tehran ta sanar da cewa mashigar a bude take ga jiragen kasuwanci da ke hada kai da rundunar ruwan Iran.
A bangaren diflomasiyya kuwa, Trump ya ce Xi Jinping ya nuna aniyar taimakawa wajen tabbatar da bude mashigar Hormuz tare da alkawarin cewa China ba za ta aika wa Iran kayan aikin soja ba a yakin da take yi da Amurka da Isra’ila.
Wani masani mai suna Drew Thompson ya ce har yanzu Amurka da China na fama da rashin yarda da juna duk da tattaunawar da shugabannin biyu suka yi, yana mai cewa taron ya fi karkata ga rage rikicin diflomasiyya tsakanin kasashen biyu.
A gefe guda kuma, ana ci gaba da zagaye na uku na tattaunawa tsakanin wakilan Lebanon da Isra’ila a Washington domin kawo karshen rikicin da ke tsakaninsu duk da ci gaba da hare-haren Isra’ila a kudancin Lebanon.
Shi kuwa Trump ya ce yana son Iran ta amince da yarjejeniya cikin gaggawa, yana mai cewa hakurinsa na kara karewa yayin da tattaunawar sulhu ke ci gaba da tangal-tangal.
