Jam’iyyar APC ta dage zaben fidda gwani na ‘yan takarar majalisar wakilai da aka shirya gudanarwa yau Juma’a zuwa ranar Asabar 16 ga watan Mayu, 2026.
Sakataren yada labaran jam’iyyar, Felix Morka, ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar, inda ya ce sauran jadawalin zabukan fidda gwani na majalisar dattawa, gwamnoni da shugaban kasa ba su sauya ba.
Sabon jadawalin ya nuna cewa za a gudanar da zaben fidda gwani na majalisar dattawa ranar Litinin 18 ga Mayu, na ‘yan majalisun jihohi ranar Laraba 20 ga Mayu, yayin da na gwamnoni zai gudana ranar Alhamis 21 ga Mayu.
za a iya karanta wannan ma:https://is.gd/8WXTTT
Haka kuma APC ta tabbatar da cewa zaben fidda gwani na shugaban kasa zai gudana kamar yadda aka tsara ranar Asabar 23 ga watan Mayu.
Rahotan jaridar Daily Trust ya bayyana cewa jam’iyyar ta dauki matakin ne saboda jinkirin kammala tantance wasu masu neman takara da suka fuskanci matsaloli a yayin tantancewar su.
Majiyoyi sun ce jinkirin ya kuma shafi shirye-shiryen tura jami’an jam’iyyar zuwa jihohi domin sa ido kan zabukan fidda gwani, musamman a wuraren da za a gudanar da zaben kai tsaye.
An kuma ruwaito cewa shugabannin APC da gwamnoni na kokarin cimma matsaya ta hanyar maslaha wajen zakulo ‘yan takara, amma wasu masu neman takara sun ki amincewa da tsarin.
Rahotanni sun nuna cewa sama da mutane 821 ne suka sayi fom din takarar kujerun majalisar wakilai a karkashin APC, yayin da fiye da mutane 2,500 suka shiga tantancewa domin kujerun majalisar dattawa, gwamnoni da sauran mukamai.
A gefe guda, Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya bukaci masu neman takara da shugabannin jam’iyyar su guji rikici da siyasar gaba yayin gudanar da zabukan fidda gwani.
Tinubu ya ce jam’iyyar APC ba za ta amince da duk wani abu da zai haddasa rabuwar kai ba, yana mai gargadin masu nasara kada su nuna isa, yayin da wadanda suka fadi kuma su rungumi sakamakon cikin mutunci.
A halin yanzu, ana sa ido sosai kan manyan ‘yan majalisar wakilai da ke neman komawa majalisar karo da dama, ciki har da Kakakin Majalisar Wakilai, Tajuddeen Abbas, da Mataimakinsa Benjamin Kalu, da kuma wasu fitattun ‘yan majalisar daga Kano, Borno, Sokoto da Edo.
