DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Friday, May 15, 2026
HomeLabaraiHisbah a Kebbi ta cafke matar aure da wasu mutane 5 a...

Hisbah a Kebbi ta cafke matar aure da wasu mutane 5 a otel

Jami’an hukumar Hisbah a jihar Kebbi sun kama wasu mutane shida, ciki har da wata matar aure, bayan wani samame da suka kai wani otel da ke Birnin Kebbi kan zargin aikata ba daidai ba.

An gudanar da samamen ne a ranar 14 ga watan Mayu a wani otel da ke bayan masaukin Shugaban kasa a Birnin Kebbi, inda aka cafke maza uku da mata uku.

Daraktan Shari’a na hukumar Hisbah, Sirajo Kamba ne ya tabbatar da kama mutanen cikin wata sanarwa da ya fitar ga manema labarai a ranar Juma’a.

Ya ce hukumar ta dauki matakin ne bayan samun bayanan sirri daga jama’a game da abubuwan da ake zargin suna faruwa a wurin.

“Bayan rahotannin da muka samu daga jama’a, jami’an Hisbah sun kai samame wurin tare da kama mutanen da ake zargi,” in ji shi.

Kamba ya ce bincike ya nuna cewa daya daga cikin matan da aka kama matar aure ce, yana mai cewa hakan na nuna bukatar kara tarbiyya da tsoron Allah a cikin al’umma.

Ya kara da cewa bincike na ci gaba kuma za a dauki matakin da ya dace da dokokin hukumar da na shari’a.

Daraktan ya kuma bukaci iyaye su rika sanya ido kan harkokin ‘ya’yansu domin kauce musu daga shiga ayyukan da ke bata tarbiyya da mutuncin al’umma.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata