Dakarun Operation FANSAN YAMMA sun hallaka wasu mutane biyu da ake zargin ‘yan kungiyar Lakurawa ne yayin wani samame a karamar hukumar Tangaza ta jihar Sokoto.
Haka kuma sojojin sun kwato makamai da dabbobin da aka sace a wasu hare-hare daban da suka aiwatar a jihohin Sokoto da Katsina.
Mai magana da yawun rundunar, Laftanar Kanal Olaniyi Osoba, ya bayyana cikin wata sanarwa cewa jami’an sun kai dauki ne bayan samun rahoton cewa wasu ‘yan ta’adda na kokarin banka wa ofishin Hukumar shige da fice ta Nijeriya da ke kauyen Ruwa Wuri wuta.
Ya ce sojojin sun yi musayar wuta da maharan, inda suka samu nasarar ajalin mutanen biyu, yayin da sauran suka tsere sakamakon karfin wutar da dakarun suka yi amfani da ita.
Bayan farmakin, sojojin sun ce sun kwato bindigogi kirar AK-47 guda biyu, harsasai da kuma babur.
A wani samame na daban a karamar hukumar Jibia ta jihar Katsina, sojojin sun yi artabu da wasu ‘yan bindiga da ke tafiya da dabbobin da suka sata a yankin Danya Bakwai.
Sanarwar ta ce maharan sun yi watsi da dabbobin bayan sojoji sun bude musu wuta.
Rahotanni sun ce an kwato dabbobi 62 da aka sace, sannan aka mayar da su ga masu su a fadar shugaban gundumar Daddara da ke Jibia.
Jaridar Punch ta ruwaito Rundunar ta Operation FANSAN YAMMA ta na jaddada kudirinta na ci gaba da yaki da ‘yan ta’adda da masu garkuwa da mutane a yankin arewa rewa maso yammacin Nijeriya, tare da bukatar jama’a su rika bai wa jami’an tsaro sahihan bayanai.
