Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu ya kare sauye-sauyen tattalin arzikin da gwamnatinsa ta bullo da su, yana mai cewa Nijeriya ba za ta iya ci gaba da tafiyar da manufofin da za su lalata makomar al’umma masu zuwa ba.
Tinubu ya bayyana hakan ne yayin wata hira a taron Africa CEO Forum na 2026 da ake gudanarwa a Kigali, kasar Rwanda, a zaman da aka yi wa take “Holding the Line: Nigeria’s Reform Bet in a Fractured World.”
Shugaban Tinubu ya amince cewa sauye-sauyen sun sanya jama’a cikin wahala, amma ya ce sun zama dole domin farfado da tattalin arziki da kuma dawo da kwarin gwiwar masu zuba jari.
Ya ce cire tallafin man fetur wani mataki ne da aka dauka domin dakatar da barnar kudaden gwamnati da ya kamata a mayar wajen ci gaban kasa.
Tinubu ya kuma kare tsarin sauya haraji da gwamnatinsa ke yi, yana mai cewa kudaden shiga za a yi amfani da su wajen bunkasa ababen more rayuwa, masana’antu, samar da ayyukan yi, ilimi da lafiya.
A cewarsa, gwamnati na kokarin tabbatar da cewa alfanun sauye-sauyen sun dore tare da inganta rayuwar ‘yan Nijeriya.
Shugaban kasar ya ce akwai alamun farfadowar tattalin arziki da kuma karin sha’awar masu zuba jari daga kasashen waje.
Hakazalika ya ce gwamnatinsa za ta ci gaba da karfafa nasarorin da aka samu idan ‘yan Nijeriya suka sake ba shi dama a gaba.
Taron Africa CEO Forum na hada shugabannin kasashen Afirka, masu zuba jari da manyan ‘yan kasuwa domin tattauna hanyoyin bunkasa tattalin arziki da hadin kan nahiyar.
