DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Tuesday, September 22, 2026
HomeSiyasaYahaya Bello ya samu tikitin takarar Sanatan Kogi ta Tsakiya a APC

Yahaya Bello ya samu tikitin takarar Sanatan Kogi ta Tsakiya a APC

Tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello, ya lashe zaben fidda gwani na jam’iyyar APC domin takarar kujerar Sanatan Kogi ta Tsakiya.

Jami’in tattara sakamakon zaben, Dakta Sadiq Mohammed, ne ya bayyana hakan a ranar Litinin bayan kammala kirgen kuri’u.

A cewarsa, Yahaya Bello ya samu kuri’u 72,349 inda ya doke babban abokin hamayyarsa Ibrahim Yakubu Adoke wanda ya samu kuri’u 315.

Sauran dan takara Momoh Yusuf Obaro, ya samu kuri’u 188 a zaben fidda gwanin.

Sakamakon da aka bayyana daga kananan hukumomi biyar na mazabar ya nuna cewa Bello ya samu kuri’u 18,341 a Adavi da 10,298 a Ajaokuta.

Hakazalika ya samu kuri’u 5,146 a Ogori, kuri’u 8,943 a Okehi da kuma kuri’u 29,621 a Okene.

A bangaren Kogi ta Yamma kuwa, rahotanni sun nuna cewa sanata mai ci Sunday Karimi ne ke kan gaba yayin da ake ci gaba da tattara sauran sakamakon zaben.

Hakan ya biyo bayan janyewar wasu fitattun ‘yan takara da suka hada da Sanata Smart Adeyemi da Samuel Bamidele Aro kafin kammala zaben.

A Kogi ta Gabas kuma, rahotanni sun nuna cewa sanata mai ci Jibrin Isah Echocho na baya a sakamakon da aka samu zuwa yanzu.

An ce ya samu kuri’u biyu kacal a karamar hukumarsa ta Dekina, yayin da babban abokin hamayyarsa Dakta Joe Erico Ameh ya samu kuri’u 19,805.

Sai dai wasu daga cikin manyan ‘yan takarar da suka hada da Muritala Ajaka da Jibrin Echocho sun soki yadda aka gudanar da zaben, suna zargin cewa bai bi ka’idojin jam’iyyar APC yadda ya kamata ba.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata