Tsohon gwamnan jihar Anambra Peter Obi, ya bayyana damuwa kan shirin gwamnatin Nijeriya na kashe kusan dala biliyan 11.6 wajen biyan bashin kasar a shekarar 2026.
Obi ya bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na X a ranar Litinin, inda ya ce lamarin ya kamata ya tayar wa ‘yan Nijeriya hankali kan yadda gwamnati ke tsara kashe kudade.
Peter Obi da ke neman takarar shugaban kasa na jam’iyyar NDC ya ce babu laifi a ci bashi matukar ana amfani da shi cikin hikima domin ayyukan ci gaba.
Sai dai ya ce halin da Nijeriya ke ciki ya bambanta saboda yawancin bashin da aka karbo a baya an kashe su ne wajen abubuwan amfani na yau da kullum ba tare da ganin gagarumin ci gaba ba.
Obi ya kara da cewa wani babban kaso na bashin da ake biya yanzu gwamnatin Bola Tinubu ce ta tara, yayin da gwamnati ke ci gaba da neman karin bashin daga kasashen waje da cikin gida.
A cewarsa, gwamnatin ta karbo kusan dala biliyan 6 daga bankin First Abu Dhabi da kuma UK Export Finance ta hannun Citibank London.
Ya ce akwai kuma karin bashin dala biliyan 1.25 da ake shirin karba daga Bankin Duniya da kuma dala miliyan 516 da Deutsche Bank ta shirya.
Obi ya ce idan aka hada wadannan, sabon bashin waje da aka sani ya kai kusan dala biliyan 7.8, baya ga bashin cikin gida da gwamnati ke ci gaba da karba ta hanyar sayar da takardun gwamnati.
Ya bayyana cewa kasafin kudin 2026 ya ware naira tiriliyan 2.46 ga lafiya, naira tiriliyan 2.56 ga ilimi da kuma naira biliyan 865 domin rage talauci.
A cewarsa, jimillar kudin wadannan bangarori uku bai wuce naira tiriliyan 5.8 ba, yayin da kudin biyan bashi kadai ya kai tsakanin naira tiriliyan 17 zuwa 18.
Obi ya ce hakan na nuna yadda biyan bashi ke hana gwamnati zuba jari a bangarorin ilimi, lafiya da walwalar jama’a.
Ya kuma ce kasashe kamar Japan, Amurka, Birtaniya, Singapore da Hadaddiyar Daular Larabawa suna karbar bashi ne domin zuba jari a ilimi, lafiya, gine-gine da fasaha da ke samar da ci gaba mai dorewa.
A karshe, Obi ya ce babban abin dubawa ba wai yawan bashin ba ne, illa yadda ake amfani da kudin wajen samar da ci gaba, rage talauci da inganta rayuwar jama’a.
