DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Wednesday, September 23, 2026
HomeSiyasaYadda Fubara ya rasa goyon bayan Tinubu da APC a rikicin Ribas

Yadda Fubara ya rasa goyon bayan Tinubu da APC a rikicin Ribas

Rikicin siyasar jihar Rivers ya sake daukar sabon salo bayan wasu sababbin bayanai sun bayyana yadda Gwamna Siminalayi Fubara ya rasa goyon bayan Shugaba Bola Tinubu da kuma shugabannin jam’iyyar APC a rikicinsa da tsohon gwamnan jihar kuma ministan Abuja, Nyesom Wike.

Rahotanni daga shugabannin APC sun ce Fubara ya samu sabani da shugabancin jam’iyyar ne bayan an zarge shi da karya yarjejeniyar sulhu da aka cimma tsakaninsa da Wike domin kawo karshen rikicin siyasar jihar Rivers.

Wani jigo a APC ya bayyana cewa shugaba Tinubu ya mika tsarin siyasar Rivers gaba daya hannun Wike, kuma hakan ne ya sa jam’iyyar ba ta yi wa Fubara cikakken tarba bayan sauyawa daga PDP zuwa APC ba.

Majiyar ta ce tun bayan rikicin farko da aka yi kokarin tsige Fubara daga mukami, Tinubu ne ya shiga tsakani domin ceto gwamnan tare da ba shi shawarar ya mayar da hankali kan mulki ya bar Wike ya jagoranci harkokin siyasa a jihar.

Rahoton ya kara da cewa a lokacin sulhun an cimma yarjejeniya cewa Fubara ba zai sake neman wa’adi na biyu ba, kuma gwamnan ya amince da hakan, lamarin da ya sa Wike ke yawan cewa “yarjejeniya-yarjejeniya ce.”

Sai dai wasu makusantan Fubara sun ce ana ci gaba da shawo kansa ya kalubalanci Wike, suna gaya masa cewa shi ne gwamnan jihar kuma ya kamata ya jagoranci APC a River.

Majiyoyi sun kuma bayyana cewa APC ba ta tantance Fubara domin shiga zaben fidda gwani na gwamna ba, kuma hakan ne ya sa ya fice daga wajen tantancewar cikin fushi kafin daga baya ya sanar da janyewa daga takara.

Haka kuma an ce duk ‘yan takarar da ke goyon bayan Fubara a zaben ‘yan majalisar dokoki na jihar da na tarayya an cire su daga jerin wadanda APC ta tantance, yayin da aka bai wa Wike cikakken iko kan tsarin zaben fidda gwani a Rivers.

Duk da haka, wasu kungiyoyin matasa da dattawan yankin Kudu maso Kudu sun nuna takaicinsu kan janyewar Fubara daga takara, inda suka zargi Wike da kokarin mamaye siyasar jihar gaba daya.

Tsohon kakakin kungiyar PANDEF, Anabs Sara-Igbe, ya bukaci al’ummar Rivers su tashi tsaye domin kare makomar jiharsu, yayin da wasu shugabannin matasa na Ijaw suka bayyana cewa janyewar Fubara ta jefa magoya bayansa cikin bakin ciki da rashin tabbas game da makomar siyasar jihar.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata