DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Wednesday, July 8, 2026
HomeLabarai‘Yan sanda sun cafke masu garkuwa da mutane a Katsina tare da...

‘Yan sanda sun cafke masu garkuwa da mutane a Katsina tare da kwato N7.5m

Rundunar ‘yan sandan jihar Katsina ta kama wasu mutane shida da ake zargi da hannu wajen sace wani yaro mai shekaru takwas a cikin birnin Katsina tare da kwato Naira miliyan 7.5 daga kudin fansar da iyalansa suka biya.

Kakakin rundunar, DSP Abubakar Sadiq, ya ce an sace yaron ne ranar 13 ga Mayu, 2026, yayin da yake dawowa daga makarantar Islamiyya a Katsina.

A cewarsa, masu garkuwar sun tuntubi iyayen yaron washegari inda suka bukaci kudin fansa har Naira miliyan 50 kafin daga baya aka sasanta suka karbi Naira miliyan 17 sannan suka saki yaron.

Rundunar ta ce jami’an sabon sashen yaki da manyan laifuka ta VCRU ne suka gudanar da bincike tare da cafke mutane shida da ake zargi ranar Juma’a, 23 ga Mayu.

Wadanda aka kama sun hada da Nura Aliyu mai shekaru 39 wanda ‘yan sanda suka bayyana a matsayin jagoran kungiyar kuma makwabcin iyalan yaron, sai Abubakar Aminu, Ibrahim Muhammad, Iliyasu Sani, Abubakar Muhammad da Abdullahi Isma’il.

‘Yan sandan sun ce wadanda ake zargin sun amsa laifin tare da bayyana sunan wani abokinsu mai suna Abdul wanda har yanzu ba a kamo shi ba, yayin da ake ci gaba da nemansa.

An kuma kwato motar Peugeot 307 da babur Boxer da ake zargin an yi amfani da su wajen aikata laifin tare da wasu kayayyaki daban-daban.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Ali Fage, ya yaba da aikin jami’an tare da jaddada kudirin rundunar na yaki da garkuwa da mutane da sauran manyan laifuka a fadin jihar Katsina.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata