Mataimakin gwamnan jihar Kano, Murtala Garo, ya bayyana yawan jama’ar da suka fito a zaben fidda gwanin shugaban kasa na jam’iyyar APC a matsayin alamar sabon fata ga makomar dimokuradiyya a Nijeriya.
Garo ya bayyana hakan ne bayan kada kuri’arsa a zaben fidda gwanin shugaban kasa da APC ta gudanar ranar Asabar a jihar Kano.
A cikin wata sanarwa da mai taimaka masa kan harkokin yada labarai, Aminu Dahiru, ya fitar, mataimakin gwamnan ya yabawa mambobin jam’iyyar bisa zaman lafiya da hadin kai da suka nuna yayin gudanar da zaben.
Ya ce yadda jama’a suka fito cikin tsari ya nuna cewa mutane sun kara amincewa da tsarin dimokuradiyya tare da nuna aniyarsu ta shiga cikin harkokin shugabanci.
Garo ya ce zaben ba kawai taron siyasa ba ne, illa wata alama ce ta hangen nesa da kishin ganin Nijeriya ta samu ci gaba.
A cewarsa, ya ga mutane daga bangarori daban-daban sun hada kai domin goyon bayan shugabancin da zai kawo cigaba, hadin kai da bunkasar kasa.
Mataimakin gwamnan ya kuma bayyana cewa nasarar Shugaba Bola Ahmed Tinubu a zaben fidda gwani ta sake farfado da fata a zukatan ‘yan Nijeriya da dama.
Ya bukaci musamman matasa da su rungumi zaman lafiya, su mutunta dimokuradiyya tare da shiga harkokin siyasa domin gina kyakkyawar makomar Nijeriya.
