Shugaban Ƙasar Amurka Donald Trump ya bayyana cewa Amurka da Iran sun kai matakin karshe na cimma yarjejeniyar kawo ƙarshen rikicin Gabas ta Tsakiya, bayan shafe watanni ana rikici a yankin.
Trump ya ce an fi mayar da hankali kan yarjejeniyar da za ta buɗe mashigin ruwan Hormuz, wadda ita ce muhimmiyar hanyar jigilar man fetur da iskar gas a duniya da ta kasance a rufe sakamakon rikicin.
Ya bayyana hakan a shafinsa na Truth Social, inda ya ce an kusa kammala tattaunawar amma har yanzu ana jiran amincewar karshe daga ɓangarorin da abin ya shafa.
Sai dai ya jaddada cewa duk abin da aka cimma har yanzu yana ƙarƙashin tabbatarwa, yayin da ake cigaba da tattauna wasu muhimman batutuwa tsakanin Amurka da Iran.
Rahotanni sun nuna cewa ƙasashen Gabas ta Tsakiya da dama ciki har da Saudiyya, Qatar, Hadaddiyar Daular Larabawa, Masar, Jordan da Bahrain sun halarci tattaunawar wayar tarho da Trump.
Haka kuma ƙasashen Pakistan da Turkey sun shiga cikin tattaunawar, inda Pakistan ta bayyana shirin karɓar sabon zagayen tattaunawa nan gaba.
Rahotanni daga Iran sun nuna cewa har yanzu akwai manyan gibi a tattaunawar, musamman kan shirin nukiliyar ƙasar da Amurka ke takaddama a kai.
Bangaren Iran ya ce ana kokarin samar da “tsarin fahimtar juna” kafin a shiga cikakkiyar yarjejeniya, amma ba a cimma matsaya kan batutuwa masu muhimmanci ba.
A gefe guda, Amurka ta ce yarjejeniyar na iya haɗawa da batun tsaro da kuma dakile mallakar sinadarin uranium mai matuƙar ƙarfi da ake amfani da shi wajen makamashin nukiliya.
Haka kuma ana sa ran yarjejeniyar za ta kawo sauƙi ga kasuwannin makamashi na duniya, musamman idan aka buɗe mashigin Hormuz da ke da matuƙar tasiri ga farashin mai.
Duk da haka, ɓangarorin biyu sun bayyana cewa tattaunawar na ci gaba, kuma ana sa ran karin bayani kan yarjejeniya ta ƙarshe nan da kwanaki ko makonni masu zuwa.
