DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Tuesday, July 7, 2026
HomeSiyasaRotimi Amaechi bai da katabus a jam'iyyar ADC - Nyesom Wike

Rotimi Amaechi bai da katabus a jam’iyyar ADC – Nyesom Wike

Ministan Abuja Nyesom Wike, ya ce tsarin shugabancin jam’iyyar ADC tun da fari ya nuna cewa tsohon Gwamnan Rivers, Rotimi Amaechi, ba zai samu adalci wajen neman tikitin takarar shugaban kasa na jam’iyyar a zaben 2027 ba.

Da yake magana a tattaunawarsa da manema labarai a Abuja ranar Litinin, Wike ya ce tun da ya ga yadda aka tsara shugabancin jam’iyyar, ya san cewa yunkurin Amaechi na samun tikitin takarar shugaban kasa a ADC ba zai yi nasara ba. Ya bayyana tsarin a matsayin “tsarin Atiku dari bisa dari.”

Jaridar Punch ta ruwaito cewa Ministan ya ce da Amaechi ya nemi shawararsa, da ya ce masa kada ya shiga takarar.

Wike ya yi zargin cewa nadin tsohon shugaban majalisar dattawa, David Mark, a matsayin shugaban ADC alama ce cewa tsarin zai fifita tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar.

Ya kara da cewa Amaechi ya kasa fahimtar yadda yanayin siyasar yake, kuma ya bari yawan sukar gwamnatin shugaba Bola Tinubu ya rinjayi shawarar da ya yanke na shiga takarar.

Ministan ya kuma sake tuno da korafe-korafen da ya yi bayan zaben fidda gwani na jam’iyyar PDP a shekarar 2022, inda ya zargi David Mark da kasa tabbatar da adalci a zaben da ya bai wa Atiku tikitin takarar shugaban kasa na jam’iyyar.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata