DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Wednesday, July 8, 2026
HomeLabaraiCutar kwalara ta yi ajalin sama da mutane 40 a Borno

Cutar kwalara ta yi ajalin sama da mutane 40 a Borno

Wata annobar kwalara ta yi sanadin mutuwar sama da mutum 40 tare da kama fiye da mutum 3,000 a kananan hukumomi bakwai na jihar Borno, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

A cewar alkaluman gwamnati, an samu wadannan mace-mace da kamuwa da cutar ne tsakanin 1 zuwa 28 ga watan Mayun 2026 a kananan hukumomin Maiduguri, Jere, Mafa, Konduga, Monguno, Ngala da Magumeri.

Sai dai iyalan wasu daga cikin masu fama da cutar da Daily Trust ta zanta da su sun ce adadin na iya zarce haka, suna masu cewa har yanzu akwai marasa lafiya da dama da ke mutuwa a gidajensu ba tare da an kai su cibiyoyin lafiya ba.

A ranar Asabar, 30 ga Mayu, gwamnatin jihar Borno ta bayyana cewa annobar kwalara ta kashe mutum 37 tare da kama sama da mutum 3,000.

Wannan na zuwa ne kwanaki uku kacal bayan wani rahoton kididdigar yaduwar cututtuka ya nuna cewa mutum 27 sun mutu yayin da mutum 2,715 suka kamu da cutar tsakanin 1 zuwa 27 ga Mayun 2026.

Saboda haka, a hukumance, adadin mace-macen ya karu da mutum 10, yayin da aka samu karin mutum sama da 285 da suka kamu da cutar cikin kwanaki uku kacal.

Bayanan sun nuna cewa yankin birnin Maiduguri ne ya fi fama da matsalar, inda fiye da rabin wadanda suka kamu da cutar suke zaune.

Wakilin jaridar da ya kai ziyara wuraren da annobar ta fi kamari da kuma cibiyoyin kula da masu fama da kwalara a Maiduguri da Jere ya gano cewa cibiyoyin sun cika da marasa lafiya fiye da yadda suke iya dauka.

Da aka tuntubi ofishin kungiyar likitoci ta kasa da kasa da ke Maiduguri, wanda ke taimakawa wajen dakile annobar a cibiyar kula da masu cutar kwalara, jami’an ofishin sun ki yin karin bayani, inda suka bukaci a aike musu da bukatar ta hanyar imel kafin su bayar da sabbin bayanai.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata