DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Monday, September 21, 2026
HomeLabaraiSERAP ta kai NNPCL ƙara kan zargin kashe N5.9bn wajen sauya suna

SERAP ta kai NNPCL ƙara kan zargin kashe N5.9bn wajen sauya suna

Ƙungiyar SERAP mai fafutikar tabbatar da gaskiya da adalci ta kai ƙara kotu kan Kamfanin Mai na Ƙasa, NNPCL, tana neman a bayyana yadda aka kashe kusan Naira biliyan 5.9 wajen sauya NNPC zuwa NNPCL.

Kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito, SERAP ta ce NNPC ta kashe Naira biliyan 2.9 daga kuɗaɗen sayar da man fetur domin aikin sauya tsarin kamfanin, yayin da kamfanin NAPIMS ma ya ware wani Naira biliyan 2.9 daga kuɗaɗen ɗanyen mai kan wannan aiki, lamarin da ya kai jimillar Naira biliyan 5.9.

Kungiyar ta buƙaci Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta tilasta wa NNPCL bayyana cikakken bayani kan yadda aka kashe kuɗin, sunayen kamfanonin da suka yi aikin, da kuma jami’an gwamnati da suka amince da fitar da kuɗaɗen.

A cikin ƙarar mai lamba FHC/ABJ/CS/1248/2026, SERAP ta ce Kwamitin Majalisar Dattawa kan Asusun Jama’a ya taɓa bayyana damuwa kan wannan kashe kuɗi, yana mai cewa adadin ya yi yawa kuma yana buƙatar ƙarin bincike da bayani a madadin jama’a.

SERAP ta ƙara da cewa ‘yan Nijeriya na da haƙƙin sanin yadda aka kashe kuɗaɗen gwamnati da ko an bi dokokin saye da gudanar da ayyukan gwamnati.

Ƙungiyar ta kuma ce rashin bayyana cikakken bayani kan wannan kashe kuɗi na nuna matsalar rashin gaskiya da riƙon amana a harkokin gudanarwar kamfanin. Har zuwa yanzu dai ba a sanya ranar sauraron ƙarar ba.

Ukashatu Wakili
Ukashatu Wakilihttps://dclhausa.com
Ukashatu Wakili is a journalist and media professional serving as Deputy Managing Editor and Internship Coordinator at DCL Hausa. He has extensive experience in broadcast and digital journalism, with expertise in news reporting, editorial production, newsroom coordination and journalist training. He holds a B.Sc. in Mass Communication from Usmanu Danfodiyo University, Sokoto.
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata