Wani likitan Nijeriya kuma mai wayar da kan jama’a kan al’amuran kiwon lafiya, Chukwuma Okoro, wanda aka fi sani da Aproko Doctor, ya yi gargaɗin cewa amfani da ruwan burtsatse (borehole) da ba a tace shi ba wajen kurkure baki na iya jefa mutum cikin haɗarin kamuwa da ƙwayoyin cuta da ke haifar da ciwon gyambon ciki (ulcer).
Jaridar Punch ta ruwaito cewa Aproko Doctor ya bayyana hakan ne a cikin wani bidiyo da ya wallafa a shafinsa na dandalin X a ranar Litinin, inda ya buƙaci mutane da su kula da tushe da tsaftar ruwan da suke amfani da shi wajen wanke baki, musamman ruwan rijiyoyin burtsatse.
Likitan ya bayyana cewa ruwan da ba a tace ko sarrafa shi ba ana iya samun ƙwayar cuta mai suna Helicobacter pylori, wadda aka fi sani da H. pylori, wadda ke da alaƙa kai-tsaye da cutar gyambon ciki. Ya ce wannan ƙwayar cuta na shiga cikin ciki ne ta lalata kariya ta musamman da ke jikin bangon ciki, lamarin da ke ba sinadarin asid damar lahanta naman ciki har ya jawo gyambo.
Cibiyar kula da cututtukan ciki da ƙoda ta ƙasar Amurka (NIDDK) ta tabbatar da cewa ƙwayar cutar H. pylori da kuma yawan shan magungunan rage zafi da kumburi na dangin NSAIDs irin su ibuprofen da naproxen na daga cikin manyan abubuwan da ke haifar da gyambon ciki. Cibiyar ta kuma bayyana cewa cutar na iya yaduwa ta hanyar abinci ko ruwan da ya gurɓata da amai, bayan gida, ko miyau na mai ɗauke da ita.
Aproko Doctor ya ƙara da cewa ana samun gurɓacewar ruwa a lokutan da bututun da ke ɗauke da ruwan burtsatse ke kusa da magudanar ruwan kashi (soakaway), inda ƙwayoyin cuta ke iya tsallakawa zuwa cikin bututun ruwan sha.
A dalilin haka, ya shawarci al’umma da su riƙa tafasa ruwa, tace shi yadda ya kamata, ko amfani da magungunan kashe ƙwayoyin cuta kafin amfani da shi wajen kurkure baki. Ya kuma yi gargaɗi kan shan magungunan rage zafi ba bisa ƙa’ida ba, shan barasa, da kuma shan sigari, tare da jan hankalin mutane da kada su yi biris idan suka ga bayan gidansu ya koma baƙi ƙirin kamar kwalta, domin hakan na iya nuna zuban jini a cikin hanji.
