DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Monday, September 21, 2026
HomeLabarai'Muradun Nijeriya ne za su jagoranci tattaunawarmu a taron UNGA'

‘Muradun Nijeriya ne za su jagoranci tattaunawarmu a taron UNGA’

Mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima, ya bayyana cewa muradun ƙasa da ci gabanta ne za su zama jagora ga dukkan tattaunawa da hulɗar da Nijeriya za ta yi a zama na 81 na babban taron majalisar ɗinkin duniya (UNGA).

Kamfanin dillancin labarai na Nijeriya (NAN) ya ruwaito cewa Shettima ya bayyana hakan ne jim kaɗan bayan isarsa birnin New York na ƙasar Amurka, inda ya je wakiltar Shugaba Bola Ahmed Tinubu a babban taron da ke gudana.

Mataimakin shugaban ƙasar ya isa New York ne tare da gwamnan jihar Rivers, Siminalayi Fubara; ƙaramar ministar kasafin kuɗi da tsare-tsaren tattalin arziki, Dr. Doris Uzoka-Anite; da kuma sauran manyan jami’an gwamnatin tarayya.

Shettima ya sake nanata aniyar Nijeriya ta yin aiki tare da sauran ƙasashen duniya, tare da jaddada kiran da Shugaba Tinubu ke ci gaba da yi na a yi garambawul ga cibiyoyi da hukumomin ƙasa da ƙasa domin su dace da yanayin tattalin arziki da yawan al’ummar duniya a yau.

“Saƙonmu a New York a bayyane yake; Nijeriya ta yi imani da haɗin gwiwar ƙasashe, sai dai ya zama wajibi hukumomin da ke kula da harkokin duniya su zama masu wakiltar kowa, masu adalci, da kuma dacewa da halin da ake ciki a yau. Za mu tattauna da abokan hulɗarmu tare da tsayin daka kan muradun Nijeriya, don ciyar da kiran da Shugaba Tinubu ya yi na samar da tsarin duniya da zai bai wa ƙasashe masu tasowa murya mai ƙarfi da dama ta samun wadata.”

NAN ta ruwaito cewa da isarsa birnin na New York, gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu; mataimakin shugaban ma’aikatan fadar shugaban ƙasa, Sanata Ibrahim Hadejia; da ministar harkokin waje, Jakada Bianca Odumegwu-Ojukwu ne suka tarbi Shettima.

Sauran jami’an da suka tarbe shi sun haɗa da ministar harkokin mata, Imaan Sulaiman-Ibrahim; ministan bunƙasa ma’adanai, Dele Alake; wakilin dindindin na Nijeriya a majalisar ɗinkin duniya, Amb. Jimoh Ibrahim; da sauran jami’an diflomasiyya.

Ana sa ran mataimakin shugaban ƙasar zai gabatar da jawabin Nijeriya yayin babban zauren mahawara, inda zai fayyace matsayar ƙasar kan manyan batutuwan ƙasa da ƙasa.

Haka kuma zai halarci tarurruka na musamman da kuma ganawa da shugabannin ƙasashe, ƙungiyoyin duniya, da abokan ci gaba domin neman sauye-sauye a tsarin hada-hadar kuɗi na duniya da kuma shirin ci gaba mai dorewa.

Ukashatu Wakili
Ukashatu Wakilihttps://dclhausa.com
Ukashatu Wakili is a journalist and media professional serving as Deputy Managing Editor and Internship Coordinator at DCL Hausa. He has extensive experience in broadcast and digital journalism, with expertise in news reporting, editorial production, newsroom coordination and journalist training. He holds a B.Sc. in Mass Communication from Usmanu Danfodiyo University, Sokoto.
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata