DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Monday, September 21, 2026
HomeLabarai'Yan bindiga sun hallaka mai tabin hankali da mutum biyu a Sokoto

‘Yan bindiga sun hallaka mai tabin hankali da mutum biyu a Sokoto

‘Yan bindiga sun kashe mutum uku tare da yin garkuwa da wasu mutum 28 yayin wani hari da suka kai a garin Kagara da ke ƙaramar hukumar Goronyo a jihar Sokoto a daren ranar Asabar.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa harin, wanda ya fara da misalin ƙarfe 8:58 na dare, ya ɗauki kusan sa’o’i uku ana fafatawa, inda mazauna garin suka bayyana cewa maharan sun ci gaba da harbe-harbe har zuwa misalin ƙarfe 12:00 na dare.

Ɗaya daga cikin waɗanda aka kashe shi ne Abdullahi Lawwali, wani mutum mai fama da taɓin hankali wanda a cewar wani mazaunin garin ya taɓa karɓar magani a asibitin masu tabin hankali na tarayya da ke Kware a jihar Sokoto. Mazaunin ya ce an harbe Lawwali ne bayan ya ƙi yarda ya bi maharan a lokacin da suka yi yunƙurin yin garkuwa da shi, sannan kuma sun sace wasu mutum bakwai daga gidansa.

Wani mazaunin garin da aka sace ‘yan uwansa ya bayyana cewa ya tsallake rijiya da baya ta hanyar ɓuya lokacin da maharan suka shigo garin. Ya ce bayan ya dawo gida da misalin ƙarfe 12:00 na dare ya tarar an tafi da mutum shida daga iyalansa, ciki har da matarsa Hassana, surukarsa Marliyya, ɗansa Atiku, ‘ya’yansa mata Jamila da Amina, da kuma ‘yar maƙwabcinsa mai suna Yajja. Sai dai ya ce daga baya an sako matarsa da ‘ya’yansa mata biyu.

Wani mazaunin garin ya bayyana cewa maharan sun yi garkuwa da mutum 28 a lokacin harin, amma daga baya suka saki mutum 10 da suka dawo gida a safiyar ranar Lahadi, sannan aka saki wasu mutum biyu da rana, wanda hakan ya sa adadin waɗanda ke tsare a hannun maharan ya rage mutum 16.

Mazauna garin sun bayyana sunayen mutum uku da aka kashe da suka haɗa da Ummaru Gobir, Lawwali Idi na Abu, da Abdullahi Lawwali, yayin da Lawwali Musa da wasu mutum biyu suka samu raunukan harbin bindiga kuma suna karɓar magani a asibitin Goronyo. Al’ummar yankin sun yi kira ga hukumomi da su tura ƙarin jami’an tsaro zuwa Kagara domin kare su daga hare-haren gaba.

Da aka tuntuɓe shi, mai magana da yawun rundunar ’yan sandan jihar Sokoto, DSP Ahmad Rufai, ya tabbatar da cewa an kashe mutum uku tare da sace mutum tara a yayin harin. Sai dai ya bayyana cewa dukkan mutum tara da aka sace sun samu nasarar tserewa daga hannun maharan, yayin da aka tsinto gawar mutum ɗaya a wurin da lamarin ya auku.

Ukashatu Wakili
Ukashatu Wakilihttps://dclhausa.com
Ukashatu Wakili is a journalist and media professional serving as Deputy Managing Editor and Internship Coordinator at DCL Hausa. He has extensive experience in broadcast and digital journalism, with expertise in news reporting, editorial production, newsroom coordination and journalist training. He holds a B.Sc. in Mass Communication from Usmanu Danfodiyo University, Sokoto.
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata