Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta kama wasu matasa maza da mata a wasu sassan birnin Kano yayin wani samammen aiki da ta gudanar karkashin shirin “Operation Kauda Badala.”
An gudanar da aikin ne a yankunan Alkanamy Suite, Buk Road da unguwar Dan-Bare da Layin Shisha, inda aka cafke matasan maza 6, mata 10 da ake zargin suna aikata dabi’un da suka sabawa tarbiyya.
Mataimakin Kwamandan Hisbah na Jihar Kano, Dr. Mujaheed Aminuddeen, ya ce wannan ne karo na farko da aka kama yawancin matasan da laifin makamancin haka.
A cewarsa, hukumar na fifita hanyar nasiha da gyaran hali, inda ake mika wadanda aka kama ga iyayensu tare da karbar alkawarin cewa ba za su sake shiga irin wadannan ayyukan ba.
DCL Hausa ta ruwaito cewa Hisbah ta jaddada aniyarta na ci gaba da yaki da duk wani abu da ke barazana ga tarbiyya da kyawawan dabi’u a jihar Kano.
