DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Tuesday, July 7, 2026
HomeLabaraiTsofaffin sojoji sun bukaci gyaran tsaro a Nijeriya

Tsofaffin sojoji sun bukaci gyaran tsaro a Nijeriya

Tsofaffin hafsoshin sojin Nijeriya sun yi kira ga gwamnati da ta sake fasalin tsarin tsaron ƙasa bayan mutuwar Manjo Janar Rabe Abubakar, wanda ya rasu bayan da ‘yan bindiga suka sace shi a jihar Katsina.

Wannan kira ya fito ne yayin wani taron manema labarai da aka gudanar a Kaduna, inda Birgediya Janar Isma’ila Abdullahi ya yi magana a madadinsu, da kuma masu alaka da marigayin.

Abdullahi ya bayyana mutuwar Janar Rabe a matsayin babban abin takaici da ke nuna irin matsalolin tsaro da ke kara ta’azzara a sassan Nijeriya.

Ya ce lamarin ya sake bayyana irin kalubalen da gwamnatin Nijeriya ke fuskanta wajen kare rayuka da dukiyoyin al’umma.

Ya yaba da kokarin gwamnatin tarayya da ta jihar Katsina wajen ceto matar marigayin, Hajiya Amina Rabe Abubakar, amma ya jaddada cewa akwai bukatar daukar karin matakai masu karfi domin magance matsalolin garkuwa da mutane, ta’addanci da kuma ayyukan ‘yan bindiga.

Tsofaffin hafsoshin sun yi gargadin cewa bai kamata a mayar da matsalar tsaro batun siyasa ko kabilanci ba, suna masu cewa matsalar ta shafi daukacin ‘yan Nijeriya ne kuma tana bukatar hadin kai wajen magance ta.

Sun bukaci a kara karfafa hukumomin tsaro, musayar bayanan sirri tsakanin jami’an tsaro da kuma daukar matakan dakile shigowar makamai ba bisa ka’ida ba ta kan iyakokin kasar.

Haka kuma sun bukaci a bai wa kungiyoyin tsaron al’umma da masu sintiri na gari horo da kayan aiki na zamani domin su taimaka wajen kare kauyuka da yankunan karkara da ke yawan fuskantar hare-haren ‘yan bindiga.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata