DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Tuesday, September 15, 2026
HomeSiyasaSowore zai ci gaba da zama a gidan gyaran hali har zuwa...

Sowore zai ci gaba da zama a gidan gyaran hali har zuwa 30 ga Yuni

Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta dage hukunci kan buƙatar da ɗan gwagwarmaya Omoyele Sowore, ya shigar na soke umarnin janye belinsa, tare da ci gaba da tsare shi har zuwa ranar 30 ga Yuni, 2026.

Lauyan Sowore, Raphael Adakole, ya gabatar da buƙatar ne a zaman kotun na ranar Laraba, inda ya roƙi kotun ta soke umarnin da ta bayar a ranar 16 ga Yuni na janye belin Sowore da kuma bayar da sammacin kama shi, saboda rashin halartar kotu.

Sai dai lauyan hukumar DSS Akinkolu Kehinde SAN, ya bukaci kotun ta yi watsi da buƙatar.

Alƙalin kotun, Mai Shari’a Mohammed Umar, bayan sauraron ɓangarorin biyu, ya ɗage yanke hukunci zuwa ranar 30 ga Yuni.

Haka kuma ya ƙi amincewa da buƙatar da lauyan Sowore ya yi ta a saki wanda yake karewa kafin ranar yanke hukunci.

Tun da farko, kotun ta ba da umarnin a tsare Sowore a gidan gyaran hali na Kuje bayan ta yi watsi da buƙatarsa ta sauya alkali daga shari’ar bisa zargin nuna son kai.

Ana tuhumar Sowore ne da zargin wallafa saƙonnin da ake cewa sun ƙunshi bayanan ƙarya kan Shugaban Kasa, Bola Ahmed Tinubu, a shafukansa na X da Facebook, zargin da DSS ke tuhumarsa da shi.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata